Ghana ta agaza wa kakashen da ke fama da Ebola

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya aike da gudunmuwar  kayayyakin masarufi zuwa  kasashen Afirka ta Yamma uku da ke fama da annobar Ebola.Ya bayar da gudunmuwar ne a madadin gwamnati da al’ummar kasar Ghana yayin wata ziyarar yini guda a kasashen Laberiya da Saliyo da kuma Guinea, ranar Litinin da ta gabata.Wannan ziyarar ta […]

Ghana ta agaza wa kakashen da ke fama da Ebola
Ghana ta agaza wa kakashen da ke fama da Ebola

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya aike da gudunmuwar  kayayyakin masarufi zuwa  kasashen Afirka ta Yamma uku da ke fama da annobar Ebola.
Ya bayar da gudunmuwar ne a madadin gwamnati da al’ummar kasar Ghana yayin wata ziyarar yini guda a kasashen Laberiya da Saliyo da kuma Guinea, ranar Litinin da ta gabata.
Wannan ziyarar ta baiwa Shugaba Mahama wadda kuma shi ne Shugaban kungiyar Tattalin Arzikin kasashen Afirka ta Yamma wato (ECOWAS), damar zantawa da takwarorinsa shagabanin kasashen don hada hannu  wajen kawo karshen annobar.
Shugaban ya fara isa ne birnin Monrobiya na kasar Laberiya, inda ya gana da Shugaban kasar Ellen Johnson Sirleaf a asirce. Daga nan ya garzaya zuwa kasar Saliyo, kafin ya karkare ziyararsa a kasar Guinea.
A lokacin da ya zanta da  manema labarai, Shugaba Mahama ya bayyana damuwarsa game da “jinkirin da kugiyoyin ba da agaji ke yi wurin cika alkawarurrukansu na tallafawa gwamnatotin kasashen da cutar ta addaba,”inji shi.
Shugabanin kasashen uku suma sun nuna farin cikinsu game da wannan ziyarar ba.