Ghana ta doke Koriya ta Kudu a Gasar Kofin Duniya
Yanzu haka Ghana na da maki 3 a teburi, a matsayi na biyu.
Ghana ta samu nasarar doke Koriya ta Kudu a ci gaba da wasannin Gasar Kofin Duniya da ke gudana a kasar Qatar.
Wannan gagarumar nasarar ta farfado da damar da Ghana ke da ita ta zuwa zagaye na gaba, muddin kasar ta samu nasara a wasanta na karshe da za ta fafata da Uruguay.
- Chelsea ta dauki Christopher Nkunku daga Leipzig
- Sojoji sun ceto mutum 9 daga hannun ‘yan bindiga a Kaduna
Mohammed Salisu ya fara jefawa Ghana kwallo a wasan, yayin da Mohammed Kudus ya jefa ta biyu a zagaye na farko.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Koriya ta Kudu ta farke ci biyun ta hannun dan wasanta Cho Gue-sung, abin da ya jefa fargaba tsakanin magoya bayan kasar Ghana.
A minti na 68 Mohammed Kudus ya jefa kwallo ta 3, abin da ya bai wa Ghana nasara, duk da yake ‘yan kasar Koriya ba su yi kasa a gwiwa ba, sakamakon munanan hare-haren da suka yi ta kaiwa har zuwa lokacin tashi a wasan.
Yanzu haka Ghana na da maki 3 a teburi, a matsayi na biyu, yayin da Portugal ke sahun gaba da maki 3, kafin karawar da za ta yi da Uruguay a yammacin ranar Litinin.
Ganin irin wadannan munanan hare-hare, hankalin magoya bayan Ghana ya tashi, musamman yadda alkalin wasa ya kara mintina 10 kafin ya tashi wasan.