Ghana ta doke Najeriya a gasar dafa shinkafa dafa-duka
A karon farko kasar Ghana ta lashe gasar iya dafa shinkafa dafa-duka da aka gudanar a tsakanin Najeriya da Ghana a dandalin taro na Cressal Park da ke birnin Accra. Wani rahoto da sashin Hausa na BBC ya wallafa a Intanet, ya bayyana yadda gasar ta kasance a tsakanin kasashen biyu wato Najeriya da Ghana. […]
A karon farko kasar Ghana ta lashe gasar iya dafa shinkafa dafa-duka da aka gudanar a tsakanin Najeriya da Ghana a dandalin taro na Cressal Park da ke birnin Accra.
Wani rahoto da sashin Hausa na BBC ya wallafa a Intanet, ya bayyana yadda gasar ta kasance a tsakanin kasashen biyu wato Najeriya da Ghana. Da ma wannan batu ya jima yana jawo ce-ce kuce a shafukan sada zumunta kan wace kasa ce tafi iya girka shinkafa dafa-duka.
A wannan karo Kamfanin Kayayyakin girki na Onga ne ya raba gardama, yayin da ya shirya gasar domin zaben gwana a cikin kasashen biyu.
Madam Sika daga kasar Ghana ce ta lashe gasar inda ta samu kyautar tsabar kudi har Dalar Amurka 2000 (kimanin Naira dubu 720).
Shinkafa dafa-duka nau’in abinci ne mai farin jini a kasashen Nahiyar Afirka da dama.
Akwai dadaddiyar hamayya ta raha a tsakanin Najeriya da Ghana a kan wace kasa ce a cikinsu dafa-dukarta ta fi dadi, musamman a kafafen sada zumunta.
Wadanda suka shirya gasar sun ce sun yi ne don kyautata alaka a tsakanin kasashen biyu kuma suna fata gasar ta dore a gaba.