Ghana ta gabatar da kasafin kudin badi
A ranar Juma’ar makon jiya ne Ministan Kudin kasar Ghana Seth Terkper ya gabatar da kasafin kudin badi.Sai dai ba kamar yadda ’yan adawa NPP sua zata ba, jawabin ministan ya nuna cewar tatalin arzikin kasar ya fara farfadowa.Gwamnatin kasar ta samu tallafin da zai ba ta kwarin gwiwar zantar da shirin ilimi kyauta a […]
A ranar Juma’ar makon jiya ne Ministan Kudin kasar Ghana Seth Terkper ya gabatar da kasafin kudin badi.
Sai dai ba kamar yadda ’yan adawa NPP sua zata ba, jawabin ministan ya nuna cewar tatalin arzikin kasar ya fara farfadowa.
Gwamnatin kasar ta samu tallafin da zai ba ta kwarin gwiwar zantar da shirin ilimi kyauta a matsayin babban makarantan sakandare wato SHS, inda dalibai 320,488 za su amfana, kamar yadda ministan ya bayyana.
“Gwamnati na kan hanyar samar da manyan makarantun unguwani har guda 200. Kuma tuni an yi nesa a aikin makarantun 123 wadanda Shugaba John Dramani Mahama ya fara kaddamarwa,” inji shi.
Har ila yau, ya ce a makon gobe ne shuagaban zai kaddamar da sabuwar Jihar bolta domin tabbatar da samar da ilimi kyauta.