Ghana za ta yi wa yara miliyan 6 allurar rigakafin Polio

A ranan Asabar da ta gabat a ne  Ministan Ma’aikatan Kiwon Lafiyar kasar Ghana ya ba da sanarwa cewa kimanin yara miliyan shida za a yi wa aluran rigakafin cutar shan-inna (Polio) a bana.Dokta Kweku Agyeman Mensah ya ce an kiyasce aikin zai ci kudi kimanin Sidi miliyin takwas kuma za’a gudanar da shi ne […]

Ghana za ta yi wa yara miliyan 6 allurar rigakafin Polio
Ghana za ta yi wa yara miliyan 6 allurar rigakafin Polio

A ranan Asabar da ta gabat a ne  Ministan Ma’aikatan Kiwon Lafiyar kasar Ghana ya ba da sanarwa cewa kimanin yara miliyan shida za a yi wa aluran rigakafin cutar shan-inna (Polio) a bana.
Dokta Kweku Agyeman Mensah ya ce an kiyasce aikin zai ci kudi kimanin Sidi miliyin takwas kuma za’a gudanar da shi ne a zango biyu cikin gundumomi 216 da ke fadin kasar.
Zangon farko dai zai fara ne daga ranar 18 (jiya Alhamis) zuwa 20 ga watan Satumba. Zango na   biyu kuma daga ranar 30 ga watan Oktoba zuwa 1 ga watan Nuwamban bana. Yayin da take kaddamar da ranar alluran rigakafin cutar ta bana, Dokta Zakaria Hafsa wanda ta karanta jawabin a madadin ministan ,ta ce rigakafin zai kiyaye yara masu kasa da shekara biyar daga kamuwa da cutar.
Ministan ya ce duk da irin nasarorin da kasar ta samu na kasancewa cikin sawun kasashen da babu cutar a cikinsu, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyanar a shekarar 2008. Har ila yau, ana bukatar kara himmatuwa in lalle ana muradin Ghana ta dawwama a hakan, ba tare da sake samun bullar sabbin wadanda suka kamu da cutar ba. Ya kuma gode wa kungiyar WHO da Asusun Taimaka wa Yara na Majalisar dinkin Duniya wato (UNICEF) da kungiyar Rotary International da sauran kungiyoyi, dangane da tallafa wa wannan gangamin da suke yi. Dokta Mensah ya ce kasar Ghana ba ta samu rahoton wani da ya kamu da cutar ba cikin shekara biyar da suka wuce, amma yadda cutar ke dada yaduwa a wasu kasashe makwabta zai iya jefa kasar cikin hatsarin yiwuwar bullarta a kowane lokaci.
Masu aikin sa-kai akalla guda 50,000 da aka ba su horo ne za su dinga zuwa gida-gida don bai wa yara rigakafin.
Har ila yau, ministan ya ce kasashe kamar su: Najeriya da Somaliya da Ekuatorial Guinea da kuma Kamaru ne halin yanzu suke fama da cutar a nahiyar Afirka, inda adadin wadanda suka kamu ya kai 149.