Ghari: An sauya sunan Karamar Hukumar Kunchi
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta sauya sunan Karamar Hukumar Kunchi zuwa Karamar Hukumar Ghari a hukumance.
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta sauya sunan Karamar Hukumar Kunchi zuwa Ghari a hukumance.
Sauya saunan karamar hukumar zuwa Ghari na kunshe ne cikin sanarwar da majalisar ta aike wa Sakataren Gwamnain jihar.
Sanarwar mai dauke da kwanan watan Alhamis 14 ga watan nan na Disamba, ta kara da cewa sauin a i daidai da tandakin kundin tsarin mulkin Najeria
Ghari, sabon sunan karamar hukumar, ya samo asali ne daga sunan Kogin tiga da ke kusa da yankin.
Sauyin sunan karamar hukumar zuwa Ghari na daga cikin abin da mutanen yankin suka dade suna nema a yi a hukumance.
Sai dai kawo yanzu ba mu samu bayani ba game da makomar sunan garin Kunchi — hedikwaar karamar hukumar Ghari.
Manyan yankunan karamar hukumar Ghari sun hada da Kunchi, Gwarmi, Bumai, Kasuwar Kuka, Matan Fada, Ridawa, Shamakawa, Yandadi Shuwaki, da Garin Sheme.
Karamar Hukumar ta hada mazabar dan Majalisar Wakilai da makwabataciyarta, Karamar Hukumar tsanyawa a Jihar Kano.
Sannan tana cikin kananan hukumomi da Sanatan Arewacin Kano ke wakilta, sannan tana makwabtaka da Karamar Hukumar Kazauren Jihar Jigawa.
Al’ummar Karamar Hukumar Ghari sun shahara da harkar noma kasuwan wanda suke gudanarwa a sassan daban-daban na kasar nan.