Gidaje da gonaki sun lalace sakamakon mamakon ruwan sama a Filato
Mutanen yankin sun nemi ɗauki daga gwamnatin jihar kan halin da suke ciki.
Mamakon ruwan sama ya lalata gidaje sama da 20 tare da gonaki a yankin Darwat-Jol da ke Ƙaramar Hukumar Riyom a Jihar Filato, lamarin da ya tilasta wa jama’a da dama barin gidajensu.
Ruwan saman, wanda aka yi da yammacin ranar Asabar, ya haddasa ambaliya wadda ta mamaye yankin.
- Matasa 2 sun ɓace sakamakon mamakon ruwan sama a Kaduna
- Yadda muka daƙile yunƙurin sace ɗalibai a Borno — Sojoji
Wani mazaunin yankin, Malam Damba Dang, ya ce wannan na ɗaya daga cikin ruwan sama mafi ƙarfi da aka samu a yankin cikin a ‘yan shekarun nan.
Ya ce rashin ingantattun magudanan ruwa ne suka sa ambaliyar ta yi muni.
Ya ce gidaje da dama da aka gina da laka da ciyawa sun rushe, yayin da jama’a suka rasa kayan abinci, tufafi da sauran kayayyakinsu.
Mazauna yankin sun kuma ce ambaliyar ta lalata gonaki da dama, lamarin da ya ƙara jefa al’ummar da ke dogaro da noma cikin tsaka mai wuya.
Sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Filato, hukumomin agajin gaggawa da ƙungiyoyi da su kai musu agajin gaggawa domin tallafa wa waɗanda abin ya shafa.