Gidajen man NNPC na sayar da fetur N950
Farashin lurar fetur a gidajen man NNPC da na ’yan kasuwa bayan ƙarin kuɗi
Farashin lita guda na man fetur ya ƙaru zuwa Naira 950 a gidajen man NNPC a Jihar Delta.
Gidajen man na NNPC a Jihar Taraba kuma sun ƙara na farashin litar zuwa N943, a ranar Laraba.
Aminiya ta lura cewa farashin litar fetur a gidajen man NNPC ya fara ne da N897 zuwa N950 — ya danganci inda suke a faɗin Najeriya
’Yan kasuwa kuma daga N940 zuwa N1,400 a yayin da masu sayarwa ta bayan fage (bumburutu) ke sayarwa a kan N1,100 zuwa N1,600.
- An kama masu garkuwa da mutane 11 a Kaduna
- Arewa ce matsalar kanta, maganin na hannunta — Wazirin Katsina
Gidajen man ’yan kasuwa a Jihar Taraba dai na sayar da man a jan N1,100 kowacce lita, ’yan bumburutu kuma a kan N1,300 zuwa N1,400
Wannan shi ne farashin da suka sayar da mai a ranar Labara, washegarin karin farashin da ya tayar da ƙura a Najeriya.
Amma Aminiya ta gano cewa gidajen man NNPC ba sa sayar da mai a safiyar Alhamis.
Gidajen man NNPC a Jihar Nasarawa na sayar da litar fetur a kan N1,100, masu bumburutu kuma N1,300 zuwa N1,400 sai dillalai a kan N1,100.
Gidajen mai a Jihar Gombe, ana sayarwa N930 a gidajen NNPC, Gombe, inda dillalan ke sayarwa N980 sauran kuma N1,050.
A Jihar Kaduna kuma gidajen man NNPC na sayar da lita a kan N904, gidajen man manyan dilalan na sayarwa a kan N950.
Sauran gidajen mai na sayarwa N1,200, ’yan bumburutu kuma N1,500 suke sayar da kowace lita.
A Jihar Filato gidajen NNPC na ba da lita a kan N897 sai masu bumburutu a kan N950.
N924 ne kudin lita Jihar Borno, inda dillalai ke badawa a akn N1,100 zuwa N1,200 sai masu bumburutu, N1,400 zuwa N1,500
Rarashin litar a wurin masu bumburutu N1,500 a Jihar Katsina, inda dalillan mai ke sayarwa a kan N1,050 zuwa N1,200.
N897 ne farashin litar fetur a gidajen man NNPC a Jihar Akwai Ibom, inda ’yan kasuwa ke sayarwa N990 zuwa N1,100, sai ’yan bumburutu a kan N1,200.
Gidajen man NNPC a Jihar Delta kuma N950 suke sayar da lita a yayin da ’yan kasuwa suke sayarwa tsakanin N1,200 zuwa N1,300.
Su kuma masu sayarwa ta bayan fage (bumburutu) N1,400 zuwa N1,500 suke sayar da lita.
A Abuja ’yan bumburutu na sayar da lita a kan N1,500 zuwa N1,600, a yayin da gidajen man NNPC ke sayarwa a kan N897. Gidajen man ’yan kasuwa kuma farashin litarsu 940.