Gidan abinci ya hana masu hijabi da jallabiyya shiga cikinsa a Saudiyya
Gidan abincin dai mallakin kasar Faransa ne
Wani babban kanti ko gidan sayar da abinci da kayan kwalam da makulashe na kasar Faransa, ya hana mata masu hijabi da abaya da maza masu jallabiyya a birnin Jeddah na Saudiyya shiga cikinsa.
Sai dai masu kantin sun musanta haka, bayan da aka rika caccakar su a shafukan Intanet kan hana matan da ke sanye da hijabi ko abaya shiga.
- An kama mutumin da ke kokarin yanka filin makabarta a Gombe
- Bam ya kashe masu ibada da dama a coci a Jihar Ondo
Gidan abincin na duniya na kasar Faransa, Bagatelle, ya gamu da suka da caccaka a shafukan Intanet, bayan da labarin zargin reshen nasa na birnin Jeddah a Saudiyya ya hana mata da ke sanye da hijabi ko abaya, da kuma maza da suka sa tufafin da galibi aka san mutanen Saudiyya da sa wa kamar jallabiyya ko alkyabba, shiga cikinsa.
Jama’a da dama a Saudiyya sun fusata inda suka rika nuna bacin ransu a shafukan Intanet suna cewa, wani kamfani na waje na neman tilasta wa mutanen Saudiyya wata al’ada da ba tasu ba, abin da ya kai har wadansu ma na kiran a rufe gidan abincin.
Hukumar Gidan Abincin na Bagatelle, ta aika wa BBC wata sanarwa, wadda a cikinta take cewa, reshen nasa na Jeddah, wanda wani kamfani na Saudiyya ke tafiyarwa, bai aikata wani abu irin wannan da ake zarginsa da yi ba, na hana mata da ke sanye da hijabi ko abaya, ko kuma maza masu jallabiyya ko alkyabba shiga cikinsa.
Ta ce abin da ta yi kawai ta bi ka’idoji da tsarin wurin shakatawa na bakin teku ne kawai, wanda wuri ne na ’yan kasuwa, inda a nan reshen nasu yake.
Kuma tsarin da ainihin masu wannan wuri suka yi shi ne, wanda gaba dayan wurin shakatawar shi ma na Saudiyya ne, tsarin shi ne duk wanda ke da wuri a wajen ya bi dokar amfani da tsarin tufafin Turawa Kantin abincin na Bagatelle ya nanata cewa yana bi da kuma mutunta dokoki da al’adun mutanen duk wurin da yake da wani reshe, da suka hada da rassansa da dama da suke kasar ta Saudiyya.
Masu kantin sun ce sun ma rufe reshen nasu da ke Jeddah kusan tsawon wata biyu baya.
Wannan hayaniya da ta taso dai wata alama ce ta irin sabanin al’ada da ake cin karo da shi, a yayin da kasar ke rungumar sauye-sauye na zamani, musamman a kokarin bunkasa harkar yawon bude-ido don samun masu ziyara daga kasashen Yamma.
Daya daga cikin wuraren da hukumomin Saudiyyar ke son janyo hankalin ’yan yawon bude-idanun shi ne bakin tekunta na Maliya, inda wannan gidan abinci yake.