Gidan da Ganduje zai tare ya yi gobara

Gobarar da ta tashi a gidan da ke unguwar Nasarawa GRA, ta lalata dukiya mai tarin yawa

Gidan da Ganduje zai tare ya yi gobara

Gobara ta tashi a gidan da Gwamnan Kano mai barin Gado, Abdullahi Umar Ganduje, zai tare bayan ya sauka daga mulki.

Gobarar da ta tashi a gidan da ke unguwar Nasarawa GRA, ta lalata dukiya mai tarin yawa da ba a kai ga tantance iya kimarta.

Da yake tabbatar da hakan, kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce gobarar ta tashi ne a daren Litinin, amma an samu nasarar kashe ta kafin ta yadu zuwa sauran sassan gidan.

Sai dai ya bayyana cewa an shawo kan wutar ne tun kafin jami’an kashe gobara su isa gidan.

Wani rahoto ya ce wutar ta fara ci ne daga bangaren da ake kiwon shanu da sauran dabbobin a cikin gidan, inda ta hallaka da dama daga cikin dabbobin.

Da aka tuntube shi, kakakin gwamnan, Abba Anwar ya ce ba shi da masaniya kan lamarin saboda ba ya gari.

Amma wata majiya a gidan ta ce wutar ta tashi ne a lokacin da masu walda ke aiki a yayin da ake karasa gyare-gyare a gidan.

Majiyar ta ce Ganduje ya koma gidan tun a makon da ya gabata, gabanin mika mulki ga gwamna mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf, wanda za a rantsar a ranar Litinin 29 ga watan nan na Mayu.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano