Gidan Gwamnatin Katsina ya yi gobara

Gidan Gwamnatin Katsina ya yi gobara a safiyar Litinin.

Gidan Gwamnatin Katsina ya yi gobara

Gobara ta tashi a Gidan Gwamnatin Jihar Katsina a safiyar Litinin.

Ɓangaren da gobarar ta kama na hade ne ganin ofishin gwamnan jihar.

A cikin zauren ne gwamnan jihar yake ganawa da manyan baƙi.

Gobarar ta tashi ne a daidai lokacin da Gwamna Mallam Dikko Umaru Radda ya kai ziyara Karamar Hukumar Funtua domin halartar taron al’umma.

Aan gudanar da taron ne domin gano matsaloli da bukatun al’ummar yankin da nufin magance su.