Gidan Iccen buda baki

Masu watsattsake da buda wagagen littattafai a yaren Hau-hau wajen hawan sa batare das a-in-sa ba, na sane dacewa, Malamin gidan Iccen Buda baki, wanda ya yi shuhura kan harkokin watsattsake da buda wagaen littattafai a harshen yaren Hau-hau wajen hawan-sa batare das a-in-sa ba, ya samu lambar yabon gundumi fasa-kwanya, a daidai lokacin da […]

Gidan Iccen buda baki

Masu watsattsake da buda wagagen littattafai a yaren Hau-hau wajen hawan sa batare das a-in-sa ba, na sane dacewa, Malamin gidan Iccen Buda baki, wanda ya yi shuhura kan harkokin watsattsake da buda wagaen littattafai a harshen yaren Hau-hau wajen hawan-sa batare das a-in-sa ba, ya samu lambar yabon gundumi fasa-kwanya, a daidai lokacin da shekarun haihuwarsa suka cika babban lauje da zagaye. Don haka ya shirya ruguntsimin biki, inda muka ci, muka sha, muka yi hani’an. Uwa-uba, ya gayyato jiga-jigan al’umma, wadanda suka hada da Farfesan Salsalar Sun-sa-in-sa Yankan-saisa-saisa, wanda ya yiwo tattaki daga jam’in jama’ar jami’ar Shehu Mujaddi, da babanmu, wanda ya sauya wa Jam’in jama’ar jami’ar birnin Dabo matsugunni da sauran mashahuran mutanen da suka kasura, suka tumbatsa a harkar yaki da juhala da tabbatar da adala. 

’Yan makarantar Dodorido kada ku ce ban ambato ’yan fici-ficin masana da suka halarci wannan runguntsumin biki na Malamin gidan iccen buda baki ba. To, don kada ku ce na yi kwauron baki, ina mai sanar da ku cewa, na ga yaron can na bayan kango, wato Gizo-gizon dakin gwaggo, kuma a wannan rana bai yi rausaya ba, sai ma kazar-kazar da ya yi ta faman yi, wajen tattara makalun da iyayen al’umma suka gabatar a wajen wannan biki. Sannan Mai Alalen baitukan wakoki ya nisahadantar da al’umma, inda ya rera wa Farfesa Salsalar-sun Sa-in-sa Yankan-saisa-sai-sa da Malamin Gidan Iccen buda baki baitukan yabo.
Da na ji wadannan baituka ana rerawa, sai na kara tabbatar da kimar mutumtakar wannan gwarzo na al’umma wanda ya ci farfesun ilimi a fannin sarrafa yaren Hau-hau wajen hawan-sa ba tare da sa-in-sa ba. Ana cikin haka sai wani daga cikin gungun masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a farfajiyar Dodorido da ke cikin Amintattar Jaridar kasar Haurobiya ya roke ni kan lallai in je in yi gaisuwa a wajen farfesa. Ni kuwa ban yi kasa a gwiwa ba, sai na rankaya, ina zuwa kuwa ya miko min hannun muka cafke gaisuwa, sannan ya ce na yiwo maka sako ta cikin kurtun Magana, ni kuwa na ce,”ban gani ba,’ don haka dai na bukaci kan lallai wannan Shehun Bobo da kwambon boko a cikin yaren Hau-hau wajen hawan-sa ba tare da sa-in-sa ba, ya rika lalubata a cikin kurtun Magana na halo alalo, ko kuma ta akwatin sakonnin mashakatar lilo da tsallake-tsallakena mai lakabin “turakundodo.”
Malamin gidan Iccen Buda baki an ruwaito cewa ya kasura, ya tumbatsa a fannin batutuwan soyewar zukatan masu tunanin soyewa a birnin Tunis, can a kasar Tunusiyya. Kowa dai ya san a wannan makaranta muna da darussan Tunusiyya: Tunanin Soyayya; da Turkiyya: Turakun Tarairayar Uwa da ’ya’ya da kuma Tanzaniyya: Tunanin Zaman da babu zamaniya, musamman yadda lumana ta wanzu a yankin Mwanza da ke kasar Tanzaniyya. Kuma na gidan Iccen buda baki ya yi rawar gaban hantsi a wajen shirya majigi, inda ya fafata das u Zilla-ziyya da Zankada-ziyya da jaruman juriyya a Sandar kora nagge da karsana da bujimin Fullo.
Batu na ingarman karfen karafa, wanda babu waskiya a cikinsa, wadannan hamshakan masana da suka halarci bikin dan gidan Iccen Buda Baki, sujn baje mana sirrin nasarar rayuwar malamin, tun sa’adda da yayi fafutikar neman sani a farfajiyar kolon malam d ake Zangon Alan-guro a kwaryar birnin Dabo, har kuma ya kaiga shiga yaki da Juhala a gidan Barden Madakin Birnin Dabo,inda ya kware a fannin Bobo da kwambon bokoko. Kai na gidan Iccen Buda baki ya kwankwadi kokon ilimi. Sannan sun bayyana yadda malamin ya yi kara-kaina a nahiyar turai, inda ya ci wo taliyar Italiyawa, ya murguda baki kamar yana cin kilishi, ya kuma kanga ghilashi ya yi ta yaren Ingilishi a birnin Ingila. Malaman sun ce, na gidan Iccen Buda baki ya hau Farin-sa, inda ya yi sa-in-sa a Faransa; uwa-uba, masana sun ce, “Na-gidan Iccen Buda baki ya yi kurmusun kamusu a kasar Jamus. A dunkule, inda muka yi wa batutuwan masanan curin kan dawo, sai mu ce,’Malamin gidan Iccen Buda Baki ya yi gwagwa da agwagi a wajen fafutikar daga martabar yaren Hau-hau wajen hawan-sa ba tare da sa-in-sa ba.
Manyan masana dai sun jajjada bukatar da ake da ita a wannan lokaci, kan lallai mu yi zungur kada mu yi zugum, bisa la’akari da abin da gwarzon al’umma Malam Sa’adu Zungur ya bijiro da shi, kimanin shekaru manuniyar sama da madambaci. Kuma suka nakalto mana dabarun da suka kamata mu bi don samun aminci a cikin amanar jagorancin al’umma, tamkar dai yadda Aminin Siyasar Kanawan Dabo ya bijiro da su cikin shekarun da suka arce.
A wannan makon ina mai karkare darasin makaranta da taya malamin gidan Iccen Buda Baki murnar samun lambar yabo. Kuma na tabbatar da cewa ruguntsimin bikinsa ya kayatar. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, ina mai yi wa malamin tunin cewa, lambobin da aka jinka masa nau’uka karamin lauje ne; akwai gundumemiya da ’yar ficil, to ’yar ficil din tasa ce, ita kuwa wannan gundumemiyar tawa ce. Don haka ya hanzarta miko ta makarantar Dodorido, idan har yana son ya samu tukwicin ‘gurasa gami da masa, ga wasa-wasa a zuba a kwanon tasa, ’yan kasa su yi ta kwasa ba wani wasa.’
Malamin gidan Iccen Buda baki, ina rokon Mai-duka ya kara cicciba likafa, yadda za ta amfanar da al’umma, wajen yaki da juhala don tabbatar da adala. Haurobiyawa mu yi zungur kada mu yi zugum; mu nemi aminci a cikin amanar jan ragamar al’umma; lallai mu yi fafutikar neman makama a daidai lokacin da zabi-sonka na shekara ta dubu karamin lauje da sili da babban lauje ke karatowa, musamman ma ganin cewa ’yancin kasar Haurobiya ya girmin Malamin gidan Iccen Buda baki, amma har zuwa yau an hana gwarazan al’umma furta batutuwa adawa da masu wawa; wasu ’yan adawar kuwa sun zamto ‘adawa in babu dawa sai a shiga dawa.