Gidan mahaukata
A gidan mahaukata ne aka yi musu jarrabawa, domin a gano wadanda suka warke. Da aka nuna musu bango, aka ce su je su fita; sai kuwa suka fita da gudu, wasu su je su doki bangon su fadi, wasu su tattake ’yan uwansu. Suna cikin yin haka sai aka ga wani daga cikinsu bai […]
A gidan mahaukata ne aka yi musu jarrabawa, domin a gano wadanda suka warke. Da aka nuna musu bango, aka ce su je su fita; sai kuwa suka fita da gudu, wasu su je su doki bangon su fadi, wasu su tattake ’yan uwansu. Suna cikin yin haka sai aka ga wani daga cikinsu bai tafi ba, yana ta kallon su. Sai aka fara murna, cewa kila ya warke. Da aka tambaye shi cewa me ya sa shi bai bi su ba, sai ya amsa da cewa: “Ku kyale su su dinga haukansu, ai ni mabudin kofar yana hannuna.”
Daga Aliyu Khan BBC Azare, 07036184519