Gidan Malam Aminu Kano da abubuwan da ke ciki
Ainihin gidan da ya rayu a cikinsa an mayar da shi cibiyar tarihi mai taken Aminu Kano Living History Museum a Turance
A ranar 17 ga Afrilu, 1983 shahararren ɗan siyasa kuma jagoran ceton talakawa, Malam Aminu Kano ya rasu a gidansa da ke Gwammaja Kano.
An binne shi a cikin harabar gidan.
Kuma ainihin gidan da ya rayu a cikinsa an mayar da shi cibiyar tarihi mai taken Aminu Kano Living History Museum a Turance.