Gobara ta tashi a gidan Olusegun Obasanjo
A daren ranar Laraba ne gobara ta tashi a gidan tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo da ke unguwar Etaiko a kwaryar birnin Abeokuta a Jihar Ogun. Mutanen da ke makwabtaka da gidan Obasanjo sun kaiwa ma’aikatan gidan dauki domin kashe gobarar da ta tashi da misalin karfe 9:30 na daren ranar Laraba. Wasu da […]
Olusegun Obasanjo, tsohon Shugaban Kasar Najeriya.
A daren ranar Laraba ne gobara ta tashi a gidan tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo da ke unguwar Etaiko a kwaryar birnin Abeokuta a Jihar Ogun.
Mutanen da ke makwabtaka da gidan Obasanjo sun kaiwa ma’aikatan gidan dauki domin kashe gobarar da ta tashi da misalin karfe 9:30 na daren ranar Laraba.
Wasu da suka shaida faruwar lamarin sun danganta tashin wutar da tangardar wutar lantarki.
Daraktan hukumar kashe gobara na jihar Ogun Fatai Adefanla, ya tabbatar da abkuwar lamarin, ya ce gobarar bata cinye gidan Obasanjo ba, hasali dai ta ci wani dakin ajiya ne kawai a cikin gidan.
Ya ce, ma’ikatana hukumar sun ci karfin lamarin inda suka kashe wutar a lokacin da suka sami labarin aukuwar lamarin da misalin karfe 10 na daren.