Gidan rediyo ya sa yara 80 a makaranta a Kano

Gidan rediyon manoma na Himma Radio da ke Kano ya dauki nauyin saka yara 80 makaranta, wadanda a da ba sa zuwa makarantar a Karamar Hukumar Madobi da ke jihar.

Gidan rediyo ya sa yara 80 a makaranta a Kano

Wasu daga cikin yaran da aka mayar makarantar

Gidan rediyon manoma na Himma Radio da ke Kano ya dauki nauyin saka yara 80 makaranta, wadanda a da ba sa zuwa makarantar a Karamar Hukumar Madobi da ke jihar.

An gudanar da bikin mayar da yaran makarantar ne ranar Talata a kofar fadar Hakimin Madobi, Sale Musa Kwankwaso.

Da yake karin haske kan dalilin shirin, shugaban tashar, Isma’il Yusuf Makwarari, ya ce mataki na daga cikin shirye-shiryen hidimta wa al’umma da tashar ta assasa domin bayar da gudunmawa wajen ci gaban al’umma.

Ya kuma ba da shawarar kafa asusun tallafa wa ilimi a karamar hukumar da ake kira da zai rika tallafa wa irin wadannan yaran.

Ya ce wannan shi ne karo na biyu da gidan rediyon yake dibar adadin yara masu yawa ya mayar da su makarantar a wannan yanki kuma zai ci gaba da yin haka a matsayin wani bangare na gudunmawarsa ga ci gaban al’umma.

Hakimin na Madobi, ya yi alkawarin mayar da yara kimanin 600 makaranta domin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin.

Ya ce shi da sauran masu rike da sarautun gargajiya za su dauki nauyin mayar da yara 50 a kowace mazaba daga cikin mazabu 12 da ke karamar hukumar.

Shugaban karamar hukumar Madobi, Alhaji Sulaiman Dan Azumi, wanda kakakin majalisar karamar hukumar, Tijjani Rabi’u Kafi (kansilan mazabar Kafin Agur), ya wakilta, ya tabbatar da cewa karamar hukumar za ta bayar da gudunmawa wajen ci gaban ilimi domin ci gaban al’umma.

Shi ma Sakataran Ilimi na karamar hukumar, Lawan Sani Gora, ya yi kira ga iyaye da su sanya ido wajen tabbatar da cewa ’ya’yansu na zuwa makaranta domin samun nasarar shirin.

A ƙarshe, Hakimin Madobi ya amince da kafa asusun tallafawa ilimi a karamar hukumar tare da bayar da wa’adin watanni uku don kaddamar da shirin.

Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki kan harkokin ilimi da kuma masu rike da sarautun gargajiya na karamar hukumar Madobi.