Gidan sama ya rufta wa daliban sakandire uku a Binin

Yara uku ne ’yan makarantar sakandire suka rasa rayukansu a sanadiyyar ruftawar wani gidan sama da suka fake wa a karkashin rumfarsa, a birnin Binin, fadar mulkin Jihar EdoWadanda al’amarin ya auku a gabansu, sun ce wannan gidan sama mai hawa daya lamba daya a babban titi na zuwa makarantar sakandaren jeka-ka-dawo da ke Urora […]

Gidan sama ya rufta wa daliban sakandire uku a Binin
Gidan sama ya rufta wa daliban sakandire uku a Binin

Yara uku ne ’yan makarantar sakandire suka rasa rayukansu a sanadiyyar ruftawar wani gidan sama da suka fake wa a karkashin rumfarsa, a birnin Binin, fadar mulkin Jihar Edo
Wadanda al’amarin ya auku a gabansu, sun ce wannan gidan sama mai hawa daya lamba daya a babban titi na zuwa makarantar sakandaren jeka-ka-dawo da ke Urora cikin garin Benin, bayan daukewar ruwan sama da aka yi da yammacin ranar Juma’ar da ta gabata  da misalin karfe  hudu da kwata, inda suka ce kawai ba zato, ba tsammani wannan ginin na gidan ya yanke daga sama ya rufta kasa akan wadannan ’yan makaranta da suka fake ruwan sama awannan gidan.
Ruftawar ginin ta yi sanadiyyar mutuwar yara uku a take, yayin da biyu suka  jikkata; wadanda suka mutun din sune  Junior da Mathew ‘ya’yan  Mista Osamudiamwen Osagiede sai wata yarinya mai shekara bakwai mai suna Gift Ize Ogbeide, kamar yadda daya daga cikin iyayen yaran, Mista Osamudiamwen Osagiede ya shaida wa Aminiya
Mista Osagiede ya ce  acikin yaran da suka mutun akwai ‘ya’yansa maza guda biyu daya mai suna Junior da Mathew sai wata yarinya ‘yar makwabcinsa mai kimani shakaru bakwai mai suna Gift Ize Ogbeide da ginin ya rufta akansu.
A cikin jimami Mista Osagiede yace wadannan yara su biyu nake dasu kuma Allah da ya bani su ya sake karbesu don haka bani da ta ce wa da abinda Ubangiji ya aiko man sai hakuri daga nan sai  ya fashe da koka yayinda Shi kuma  Baban marigayiyar Gift Ize Ogbeide Sai kuka  yake ta yi ana kamashi don haka ba’a samu dama aji ta bakinsaba a lokacin. Su kuwa wadanda suka jikkata, su biyu, ba a tantance sunansu ba. Suna can dai suna jinya a gadon asibiti.