Gidan sarautar Lafogido ya janye kararsa game da sabon Ooni na Ife

Jagoran zuriyar Sooko a gidan sarautar Lafogido a masarautar Ile-Ife, tsohon Gwamnan Jihar Osun Cif Adeleke Adewoyin ya tabbatar da batun janye karar da suka shigar gaban kotu tun farko da suke kalubalantar matakin tsame gidan sarautar tasu daga fito da dan takarar sarautar Ooni da masu zaben sabon sarki da Gwamnatin Jihar Osun suka […]

Gidan sarautar Lafogido ya janye kararsa game da sabon Ooni na Ife
Gidan sarautar Lafogido ya janye kararsa game da sabon Ooni na Ife

Jagoran zuriyar Sooko a gidan sarautar Lafogido a masarautar Ile-Ife, tsohon Gwamnan Jihar Osun Cif Adeleke Adewoyin ya tabbatar da batun janye karar da suka shigar gaban kotu tun farko da suke kalubalantar matakin tsame gidan sarautar tasu daga fito da dan takarar sarautar Ooni da masu zaben sabon sarki da Gwamnatin Jihar Osun suka yi.

Cif Adewoyin ya ce: “Tun da masu zaben sabon Ooni da gwamnatin jihar sun ambaci sunan sabon sarki, to babu abin da gidan sarautar Lafogido zai iya yi sai janye karar daga kotu. Ba mu da zabi da ya wuce hada kai da sabon Ooni domin gyaran abubuwa.
“A al’adance, an hana talakawa yin fada ko jayayya da Ooni da ke kan gado. Wannan dadaddiyar magana ce da ta yi fice kuma ake yawan fadinta a masarautar Ife. Saboda haka muka shawarci lauyanmu da ya janye karar daga kotu.” Inji Cif Adewoyin, wanda ya yi fatan gwamnatin jihar da dukkan masu hannu a kan batun sarauta a masarautar Ife za su fara aikin yin gyara a game da batun tsarin karba-karba a tsakanin gidajen sarauta hudu na masarautar. Ya ce an dade da mancewa da gidan sarautarsu ta Lafogido ta fannin fito da dan takarar sabon sarki a masarautar ta Ife.
Da yake amsa wata tambaya, tsohon Gwamnan ya ce: “Za mu yi mubaya’a ga sabon Ooni, musamman domin yin aiki tare da zai kai mu ga gano irin kura-kuran da aka yi a baya; domin yin gyara da samo hanyoyin farfado da martabar wannan masarauta ta Ife, wacce uwa ce ga kabilun Yarabawa a ciki da wajen Najeriya.”
A yayin hira da ’yan jarida a Juma’ar da ta gabata, da ya isa cikin garin Ile-Ife kafin ya shige cikin dakin Ilofi da zai shafe kwanaki 21 a ciki ba tare da fitowa ko ganawa da iyalai da sauran jama’a ba, sabon Ooni na Ife, Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi, ya tabo batun jayayyar da ta- ki-ci-ta-ki-cinyewa a tsakanin al’ummomin garuruwan Ile-Ife da Modakeke da suke manne da juna, a inda ya yi bayanin cewa: “Zamani ya canza saboda haka babban aiki ne a gabanmu da ya zama wajibi mu nema wa kanmu mafita wajen ganin mun yi watsi da mummunar gaba da janyo baki da za su taimaka wajen gina masana’antu da kamfanoni a cikin masarautar Ife da za su yi mana maganin irin ukubar da ta dabaibaye al’ummarmu.”