Gidan yari zan jefa duk wanda ya karkatar da kayan tallafi —Bago

Gwamnatin Jihar Neja ta ba da hutun kwanaki uku domin rabon kayan tallafi da Tinubu ya bayar

Gidan yari zan jefa duk wanda ya karkatar da kayan tallafi —Bago

Gwamnan Jihar Neja Umar Bago ya ce duk wanda ya kuskura ya karkatar da kayan tallafin da gwamantin tarayya ta bayar a jihar, sai an daure shi a gidan yari, komai girman matsayinsa.

Gwamna Bago ya bayyana wa ’yan jarida cewa daga jami’an gwamnati zuwa sarakunan gargajiya, duk wanda aka kama ya karkatar da kayan da gwamnatin tarayya ta bayar domin rage wa talakawa halin matsin da suka shiga a sakamakon janye tallafin mai, to babu makawa gidan yari ne makomarsa.

Gwamnan ya sanar da haka ne bayan ya ba da hutun kwana uku domin ma’aikatanta su sami zuwa karbar kayan tallafin  da kudinsu ya kai Naira tiriliyan 3.6.

Ya ce hutun na ranar Laraba da Alhamis da Juma’a zai ba wa ma’aikata da masu rike da mukaman siyasa damar zuwa mazabunsu domin sanya ido da kuma tabbatar da gaskiya da adalci a wajen rabon kayan.

Don haka ya kuma bukaci ’yan jarida da malaman addini da masu sarautun gargajiya su sanya ido kan yadda za a tafiyar da rabon kayan a yankunansu domin tabbatar da cewa mutane masu karamin karfi da masu rauni sun samu.

Gwamnan ya bayyana cewa jiharsa ta samu kudi Naira biliyan biyu da motoci biyar na hatsi daga Gwamnatin Tarayya, “amma muna jiran buhu 40,000 na masara da kuma karin Naira biliyan biyu.

“Duk da haka maimakon mu yi ta jira, alhali ga halin da mutane ke ciki, mun yanke shawarar cikawa daga aljihun gwamnatin jiha, mu raba wa jama’a kafin gwamnatin tarayya ta biya mu.

“Rabon masarar kuma za mu jinkirta shi zuwa lokacin gwamnatin tarayya ta kawo,” in ji gwamnan a ranar Juma’a.

Yadda za a yi rabon

Gwamnan ya ce an kafa kwamitocin rabon tallafin a daukacin kananan hukumomi 25 da ke jihar, kuma ya ba da umarnin a raba wa mutane kayan tallafin ba tare da la’akari da kowace irin alaka ko bambaci ba.

A cewarsa, domin hana karkatar da tallafin, an ware wa masu sarautun gargajiya a fadin jihar miliyan N80, sannan ya gargade su kan taba abin da aka ware domin talakawa masu karamin karfi.

Naira miliyan 75 kuma an ware wa masu gudun hijira a fadin jihar, sai miliyan N100 ga jami’an tsaro, jam’iyyun siyasa kuma aka ware wa miliyan 150.

A cewarsa, gwamnatin jihar ta sayo masara da shinkafa ta miliyan N575 domin rabawa da nufin ganin ya kai talakawa da ake nufi.

Zuwa ranar Litinin ya ce za a ba wa kananan hukumomi kudin domin kwamitocinsu su sayo kayayyakanin da ake bukata.

Sufuri kyauta

Bago ya ce gwamnatin jihar za ta sayo manyan motocin safa guda 200 domin jigilar daliban duk kyauta a fadin jihar, ma’aikatan gwamnati kuma za a rika daukar su a kan farashi mai rahusa.

A cewarsa, guda 100 daga cikin motocin za su rika bin hanyar Minna-Suleja-Abuja; 50 kuma cikin garin Minna, ragowar 50 kuma a sauran kananan hukumomi.

Shiri bunkasa noma

Ya kuma umarci ma’aikatar aikin gona ta samar da filin noma mai girman hekta 10, 000 domin nomawa a kananan hukumomi 25 inda ya ce gwamnati za ta samar musu da taraktoci da sauran kayan aikin gona.

Bago ya ce a kashin farko na shirin, za a dauki matasa 500,000 aiki a gonakin gwamnati, sannan 400,000 za su yi aiki a gonakin a matsayin masu tara ’ya’yan kadanya, nan da shekara guda.