Gidan zumu ba kasuwa ne ba
Gwamnatin Tarayya ita ce yaya babba tsakanin gwamnatocin jihohi, kuma ita yaya tamkar uwa take mai bayar da mama. Shi ya sa tun farkon kafuwar Gwamnatin Muhamadu Buhari, kusan watanni 13 da suka gabata, gwamnonin jihohi ke garzayawa gare shi, rirrike da kokunan bara, don ya agaza musu da dan abin da za su samu […]
Gwamnatin Tarayya ita ce yaya babba tsakanin gwamnatocin jihohi, kuma ita yaya tamkar uwa take mai bayar da mama. Shi ya sa tun farkon kafuwar Gwamnatin Muhamadu Buhari, kusan watanni 13 da suka gabata, gwamnonin jihohi ke garzayawa gare shi, rirrike da kokunan bara, don ya agaza musu da dan abin da za su samu sukunin fara ayyukan fita kunyar jama’ar da suka zazzabe su. A watan Yulin shekarar bara Shugaba Buhari ya fitar da wasu kudi sama da Naira miliyan dubu dari takwas wadanda aka kacancanawa wasu gwamnonin guda 27 suka kokkoma jihohinsu, suka karkashe gararin gabansu da su. Bayan watanni tara da yin haka kuma, sai ya kara yayyafa musu wasu Naira miliyan dubu 10 da dan doriya don su gyagije, su kara murmurewa, sa’ilin da matsi ya yi matsi bayan faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya.
To amma duk da irin wannan karimcin da aka yi musu, har tashi biyu suna lakumewa, wasu gwamnonin daga cikin 27 din da suka amfana daga hangen sun kasa biyan ma’aikatansu albashinsu na watanni barkatai, sun kuma koma sun tsuttsuguna, sun zura wa Shugaba Buhari idanu don ya karo wani rancen, domin a cewarsu ai bashi bai kisa , kuma kan da babu bashi bisansa kan banza ne. To, amma duk da kasa biyan wancan rancen da gwamnonin jihohi suka yi, Shugaba Buhari bai daddara ba, alhali kuwa shi ma gwamnatinsa ta fada kwata, tana fama da matsi da kanfar kudade, amma duk da haka nan sai da ya kukuta, ya ciwo bashin wasu Naira miliyan dubu 90, a ‘yan kwanakin da suka gabata, daga wasu kamfanoni masu zaman kansu, wadanda suka yi wa kudin da suka ba shi rance inshora don gudun kada su salwanta idan ya sake bai wa gwamnonin. Shi ya sa bayan ruwa da aka dora kan rancen da za a bai wa gwamnonin na kashi tara cikin dari, aka kuma gindaya musu tsauraran sharuddan da tilas sai kowaccensu ta cika su kafin a kai ga ba ta rancen .
Akwai hikayoyi da yawa game da rancen da aka bayar ga gwamnoni har tashi biyu, wadanda ba su da dadin ji game da abubuwan da ba su kamata ba gwamnonin su aiwatar da wadancan kudaden da aka ce wai sun kece-raini da su. Wasu sun yi ta facaka da kudaden ba tare da turarrabin komai ba, suna ta tumurmusa ba kakkautawa, kamar sun samu gadon kaka-da-kakanninsu. Wasu gwamnonin kuwa sun ki kulawa ko sanya idanu kan wasu kudaden da suka bi ruwa a banza wajen biyan albashin ma’aikatan bogi, da kuma wadanda manyan jami’an gwamnatocinsu suka dinga yin sama-da-fadI da su abinsu. Sauran gwamnoni masu kamannin hawainiya ba su canja halaye da dabi’unsu na sharholiya da adankiya da dukiyar gwamnati ba, haka nan suka amayar, suka yi ta cin duniyarsu da tsinke.
To amma ko da ma akwai za’ida cikin wadannan hikayoyin game da yadda gwamnoni suka sarrafa wancan rancen da aka ba su, duk da haka nan babu laifi idan a wannan karon Gwamnati ta gindaya musu tsauraran sharudda kafin su karbi wani rancen a karo na uku don gudun kada su mayar da shi garin banza don yin farau-farau din banza da shi. Gwamnati ta kyauta da ta bukaci su dinga yin cikakken bayani a bainal-jama’a bisa abin da ya je, da kuma wanda ya zo, game da kudin da suka yi hagen su.
A bisa gaskiya gwamnati ba za ta amince, ko kuma a ce ba za ta zama tamkar Sarkin Fawa ba, wanda ke karbar rance don ya biya wani bashi. Babu hali a ce za ta dinga taimaka wa gwamnonin da ba su son taimakon kansu, domin kuwa ga albarkatu nan jibge suna kwance akai, amma ba su motsawa don tonowa. To a yanzu ya kamata gwamnonin jihohi su yunkura, su nuna wa talakawansu da kuma jama’ar Najeriya baki daya cewa su fa ba cima-zaune ne ba, suna iya cirewa kawunansu kitse a wuta, domin kuwa mutanensu sun sanya su a gaba game da haka, ba kuma za su gafarta musu ba idan suka zame wasu ladifai ko lusarai, wadanda za a dinga yi wa dariya da zunde. Tilas ne fa su nuna cewa kowane kwabo daga cikin dukiyar talakawa ya tafi bisa aikin da za a yi musu, wanda kuma za su ci moriyarsa. Dangane da haka ne za su tashi haikan wajen kwakwulo kudin shiga, su tabbatar kuma sun shige lalitar hukuma, an kuma sarrafa su ta hanya mai kyau. Tilas ne kuma gwamnoni su tashi haikan wajen yaki da rashawa a jihohohinsu da suka dade da zame wa tsumma makunshin cuta dangane da rashawa da cin hanci.
Sa’ilin da ake ganin cewa matsalolin da suka taso wa gwamnoni har suke sake bidar wani rancen don magancewa, ba za su rasa nasaba ba da rashin kan-gado wajen tsara ayyukan da suka fi muhimmanci da gaggauta aiwatar da su, maimakon shantakewa ana ta sharholiya da bankaura. Ashe ke nan tilas ne a wannan karon gwamnonin su guje wa abubuwan da za su komar da su gidan jiya, su kuma dage wajen yin aikace-aikace da take-taken da za su inganta matsayinsu na ingantattun shugabannin al’ummominsu wadanda suka dogara a kansu don tserar da su daga bala’o’i da fitintinun da suka hana su more gardin rayuwa a kasar da aka mayar da su ‘ya’yan bora alhali kuwa suna da galihu daidai da na ‘ya’yan mowa.
Kodayake ana cewa sharuddan da aka gindaya sun yi tsauri ainun, kuma ba dukkan gwamnoni ne za su iya cika su ba, idan har an bayar da rancen ga wadanda suka cancanta, a tabbatar da cewa ba a karkatar da kudin ba zuwa wasu hanyoyin da ba za su amfani talakawa ba, sa’anan kuma gwamnoni su tuna cewa kudin rancen fa talakawa ne za su biya, wasu ma har sai an kai ga jikokin-jikokinsu ba a gama biya ba. To, an ce dai bashi hanji ne, yana cikin kowa, kada gwamnonin jihohi su ga cewa Gwamnatin Buhari ita ma bashi ne take ciwowa, tana ba su, saboda haka nan za su shantake su yi ta sharholiya da ‘yan kudin da suke samu a jihohinsu ba tare da alkintawa ba, domin sun san suna da uwa a gindin murhu, ba kuma za su ci tuwonsu gaya ba. To su tuna fa ai gidan ‘Zumu ba kasuwa ce ba.’