Gidauniya ta raba wa gajiyayyu tallafin azumi a Gombe

Ana dai sa ran tallafawa magidanta 5,000 ne a karkashin shirin tallafin a watan azumi.

Gidauniya ta raba wa gajiyayyu tallafin azumi a Gombe

Gidauniyar Zakka da Wakafi ta jihar Gombe a ranar Lahadi ta raba kayayyakin masarufi don tallafa wa marasa galihu da marayu fiye da 700 a jihar.

Ana dai sa ran tallafawa magidanta 5,000 ne a karkashin shirin tallafin a watan azumi.

Shugaban gidauniyar, Ustaz Abdullahi Abubakar Lamido ne ya shaida hakan a lokacin da yake zantawa da Aminiya a yayin da suka kai tallafin ga wasu marasa galihu a Gombe.

Ya ce unguwannin da suka kai kayan tallafin sun hada da Comprehensive da Malam Inna da Kundulu da kuma gidan Marayu na AL-GUH dake unguwar Tumfure.

Yace sun so su fara raba tallafin da wuri amma hakan bai yuwu ba saboda jama’a ne ke tallafawa da gudumawar, su kuma a wannan karon an dan samu jinkiri amma dai yanzu komai ya koma yadda ya kamata.

A cewar sa, magidanta dubu biyar ne suke sa ran tallafawa, da kayan abinci buda baki da suka hada da shinkafa da suga da wake da man girki da kafi-zabo da kuma gero.

Abdullahi Lamido ya yi kira ga jama’a da su kara taimakawa wajen kawo zakkarsu da gudummawa, wacce da ita ne ake sayen kayayyakin tallafin.

Ya ce nan da dan lokaci za su ba marayu kayan sallah.

Ita dai gidauniyar ta fara bada irin wannan tallafi ne kimanin shekaru biyar da suka gabata kuma ta fi taimakawa marasa galihu da mata da suke da marayu suna koya musu sana’o’i daban-daban suna kuma basu jari kyauta.

Daga nan sai ya godewa jama’ar da suke kawo gudummawarsu wajen gudanar da wannan aikin lada tare da yin kira ga sauran masu masu hali da suma su shigo wajen ganin an fadada taimakon.