Gidauniyar Bill Gate da ta Dangote za su hada hannu don yaki da poliyo

Hamshakin mai kudin nan na duniya Bill Gate da hadin gwiwar Gidauniyar Dangote za su taimaka wajen yaki da cutar shan inna da ake kira poliyo a takaice. Bill Gate, wanda ya zo rangadi a Najeriya, ya kai ziyara Legas inda ya gana da Gwamnan Jihar Legas Babatunde Raji Fashola inda ya bayyana masa cewa […]

Gidauniyar Bill Gate da ta Dangote za su hada hannu don yaki da poliyo
Gidauniyar Bill Gate da ta Dangote za su hada hannu don yaki da poliyo

Hamshakin mai kudin nan na duniya Bill Gate da hadin gwiwar Gidauniyar Dangote za su taimaka wajen yaki da cutar shan inna da ake kira poliyo a takaice.

Bill Gate, wanda ya zo rangadi a Najeriya, ya kai ziyara Legas inda ya gana da Gwamnan Jihar Legas Babatunde Raji Fashola inda ya bayyana masa cewa Gidauniyar Bill &Milinda da taimakon Gidauniyar Dangote za su ci gaba da ba da kudi masu yawa ta yadda cikin kankanen lokaci cutar za ta zame tarihi a Najeriya da kasashen Afirka zuwa Nahiyar Asiya, “idan so samu ne ya kasance a badi Najeriya ta yi ban kwanan da cutar,” inji shi.
Bil Gate ya ce daya daga cikin hanyoyin da aka bi domin kakkabe cutar a Najeriya ita ce a inganta yekuwa ta yadda duk inda mutane suke za su san da wannan rigakafin da inda za su same ta da lokacin da za su same ta.
Ya ce idan aka shuka wannan cikin zukatan mutane, musamman wadanda suke karkara za a samu saukin karbar allurar. Mista Gate ya ce da yawa yaran da cutar ta yi musu illa, iyayensu ba su san da allurar rigakafin ba, idan kuma sun sani ba su san inda za su same ta ba, amma idan aka yunkura wajen wayar da kan jama’a zai taimaka kwarai. Ya ce yana fata lokacin da zai dawo ya ga abin da ya fi wanda ya gani a yanzu.
Da yake masa maraba, Gwamna Babatunde Fashola cewa ya yi a Jihar Legas suna bakin kokarinsu don yakar cutar, sai dai ya ce daya daga cikin hanyoyin da ya dace a yaki cutar ita ce a sanya wadanda suka sha da kyar daga cutar a ba su goyon baya ta yadda za su amfani rayuwarsu, su kasance a sahun gaba wajen yekuwar yaki da cutar.
Ya ce wadanda suka rayu bayan kamuwa da cutar za su fi kowa sanin abin da suke ji kuma idan sun fada wa jama’a za su fi saurin saurarensu, “wannan shi ne yadda nake so a bullo wa yekuwa game da yakar cutar,” inji shi.
Ya ce Gidauniyar Dangote da ta Bill Gate&Milinda da gwamnatin jihar za su samu wadanda cutar ta kassara a sanya su a gaba domin jama’a su gani a zahiri, su kuma san cewa wanda ya yi watsi da rigakafin ga abin da ka iya kasancewa a kansa.
Shi kuwa Alhaji Aliko dangote cewa ya yi za su ba da duk gudunmawar da ta kamata ga Gidauniyar Bill&Milinda domin hakarsu ta cimma ruwa. Ya ce ya amince wayar da kan jama’a na sahun farko da ya kamata a inganta domin mutane su rungumi yekuwar.
Ya ce sun je Legas ne domin sanin inda za su taimaka wa jihar wajen yaki da cutar shan inna da har yanzu ke addabar Najeriya da wasu kasashen Afirka da Asiya.