Gidauniyar bSF ta bullo da karin shirye-shiryen

Gidauniyar tallafa wa wadanda rikici ya shafa (bSF), ta kara bullo da shirye-shiryen ingantawa da farfado da rayuwar ’yan gudun hijirar Arewa maso Gabas a ci gaba da kokarin da take yi na magance kuncin da suke ciki. Za a gabatar da wasu ayyuka a jihohin da suka fi fuskantar hare-haren ’yan Boko Haram da […]

Gidauniyar bSF ta bullo da karin shirye-shiryen

Gidauniyar tallafa wa wadanda rikici ya shafa (bSF), ta kara bullo da shirye-shiryen ingantawa da farfado da rayuwar ’yan gudun hijirar Arewa maso Gabas a ci gaba da kokarin da take yi na magance kuncin da suke ciki.

Za a gabatar da wasu ayyuka a jihohin da suka fi fuskantar hare-haren ’yan Boko Haram da suka hada da Borno da Adamawa da Yobe. Kuma a karkashin wannan shiri gidauniyar ta bullo da ayyuka da dama da niyyar fadada shirin karfafa harkokin tattalin arzikin mata zuwa mata dubu biyar. Wannan shiri zai shafi matan da a baya suka ci gajiyar shirin nan ne na Bunkasa Tattalin Arzikin Mata (WEP).

A yayin gudanar da wannan kashi, matan za su tashi daga kungiyoyin bayar da ajiya da rance (SLA), zuwa kungiyoyin gama-kai domin su samu damar samun harkar kasuwanci mai kawo kudin shiga mai yawa.

Gidauniyar bSF ta kuma fara aza harsashin matakan jiha na aiwatar da shirin hadin gwiwa don rarraba kayayyakin aiki gona domin gudanar da noman rani. Kayayyakin aikin gonar da za a raba wa manoman sun hada da ingantaccen iri da maganin feshi da taki da kuma dabbobin kiwo.  Abokan hadin gwiwa da suka fito daga kungiyoyi masu zaman kansu suna aiki da wasu cibiyoyin gwamnati masu alaka tuni sun fara aikin sanya jama’a cikin shirin a matakan unguwanni. Wadannan ayyuka sun hada da zabo wadanda za su shiga shirin da adana bayanansu da karkasa su zuwa rukunoni don shirye-shiryen fara gudanar da shirin SLA. Shirin na inganta rayuwa ya kuma hada da karfafa kungiyoyi masu zaman kansu da za su horar da shugabannin rukunonin SLA. Kuma bayan wannan kashi za a biyo bayansa da kaddamar da shirin tarihi na Gidauniyar  bSF a ranar 19 ga Mayu dkan ayyukan da za ta samar da kudinsu a Bama da ke Jihar Borno, wadanda suka kai Naira miliyan 368.