Gidauniyar Dahiru Mangal ta tallafa wa marasa lafiya 30,000 a Katsina

Shirin ana gudanar da shi lokaci-lokaci, kuma Alhaji Dahiru Bara’u Mangal ne ke ɗaukar nauyin komai domin marasa galihu.

Gidauniyar Dahiru Mangal ta tallafa wa marasa lafiya 30,000 a Katsina

Taswirar Jihar Katsina

Gidauniyar Dahiru Bara’u Mangal ta bayyana cewa marasa lafiya masu ƙaramin ƙarfi sama da 30,000 ne suka amfana da shirye-shiryen ba da magani kyauta da ta gudanar a faɗin Jihar Katsina tun daga shekarar 2018.

Haka kuma, gidauniyar ta fara tantancewa da kula da kusan marasa lafiya 2,000 masu fama da cututtukan ido daban-daban, ciki har da waɗanda ke buƙatar tiyata.

Mamba a Kwamitin Amintattu na gidauniyar, Hussaini Kabir, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da shirin yi wa marasa lafiya sama da 700 tiyatar ƙaba (Hernia) da kuma Hydrocele kyauta a Babban Asibitin Katsina.

Kabir ya ce marasa lafiya sama da 700 daga sassa daban-daban na Jihar Katsina da ma wasu jihohi ne ake sa ran za su amfana da shirin tiyatar kyauta.

Ya bayyana cewa manufar shirin ita ce ƙara sauƙaƙa wa marasa ƙarfi samun ingantaccen kulawar lafiya.

A cewarsa, ana fara tantance marasa lafiyar kafin a yi musu tiyata kyauta, yayin da waɗanda ke fama da ƙananan cututtuka za a ba su magunguna ba tare da sun biya komai ba.

“Shirin ana gudanar da shi lokaci-lokaci, kuma Alhaji Dahiru Bara’u Mangal ne ke ɗaukar nauyin komai domin samar da ingantaccen kulawar lafiya ga marasa galihu.

“Duk marasa lafiyar da ke buƙatar tiyata za a yi musu kyauta, yayin da waɗanda ke da ƙananan matsalolin lafiya za a ba su magungunan da suka dace ba tare da wani kuɗi ba,” in ji shi.

Kabir ya ƙara da cewa gidauniyar na kuma ɗaukar nauyin tiyatar ido kyauta, tiyatar cututtukan mafitsara da hanyoyin fitsari (urology), da sauran ayyukan jinya na musamman a faɗin jihar.

Shi ma da yake jawabi, Dakta Saifullahi Bawale ya yaba wa gidauniyar bisa yadda take taimakawa gwamnati wajen inganta harkokin kiwon lafiya ta hanyar shirye-shiryen jinya kyauta.

Ya ce shirin ya dawo da fata ga dubban marasa lafiya marasa ƙarfi da ba su da ikon biyan kuɗin magani.

A cewarsa, an tanadi isassun likitoci, ma’aikatan lafiya, kayan aiki, magunguna da sauran kayayyakin da ake buƙata domin tabbatar da nasarar shirin.

Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da shirin sun gode wa gidauniyar, suna cewa tallafin ya sake ba su fata.

Malama Zulaihat Adamu daga ƙaramar hukumar Jibiya ta bayyana farin cikinta cewa ɗanta zai samu tiyatar ƙaba kyauta, tana mai cewa sun daɗe ba su da ƙarfin biyan kuɗin maganin.

Shi ma Shamsu Abubakar ya yabawa gidauniyar bisa ɗaukar nauyin tiyatar idonsa, tare da addu’ar Allah Ya sa wannan ya zama ƙarshen matsalar idon da yake fama da ita.

Firdausi Muhammad daga ƙaramar hukumar Batsari ta ce shirin babban sauƙi ne ga marasa lafiya da ba za su iya biyan kuɗin tiyata ba, tare da yi wa wanda ya kafa gidauniyar addu’ar Allah Ya ƙara masa albarka.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa gidauniyar na ci gaba da gudanar da shirin kula da lafiyar ido kyauta a Cibiyar Kula da Ido ta Katsina, inda ake tantancewa da ba marasa lafiya magani ba tare da biyan kuɗi ba.

Haka kuma, ana ba marasa lafiyar da ke buƙatar tabarau kyauta, yayin da waɗanda aka gano suna buƙatar tiyatar ido ake tsara musu ranar yin tiyatar ba tare da wani kuɗi ba.