Gidauniyar Gwagware ta ba ’yan gudun hijira tallafin kayan abinci
Gidauniyar Gwagware wadda Babban Daraktan SMEDAN na kasa Dokta Dikko Radda ya kafa ta bayar da tallafn kayan abinci ga ’yan gudun hijira da hare-haren ’yan fashi, barayin shanu, garkuwa da mutane da kisan gilla inda suka addabi jama’a har suka yi sanadiyar raba su da gidajen su a wasu yankunan Kananan Hukumomi a Jahar […]
Gidauniyar Gwagware wadda Babban Daraktan SMEDAN na kasa Dokta Dikko Radda ya kafa ta bayar da tallafn kayan abinci ga ’yan gudun hijira da hare-haren ’yan fashi, barayin shanu, garkuwa da mutane da kisan gilla inda suka addabi jama’a har suka yi sanadiyar raba su da gidajen su a wasu yankunan Kananan Hukumomi a Jahar Katsina.
Kamar yadda ya ce, a lokacin da yake raba buhunhunan 100 da suka hada na masara 25, gero 25, wake 25 da kuma dawa 25 ga Sarkin Ruman Katsina Hakimin Batsari Alhaji Tukur Ma’azu, Dokta Raxxa ya ce, ya zama wajibi ga duk wanda Allah ya ba hali da ya taimakawa wadannan bayin Allah wadanda aka raba da iyalansu da muhallansu bayan kashe masu jama’a, bayan kai masu hare-hare da marasa imani ke yi. Kamar yadda ya ce, Karamar Hukumar Batsari ce ta fi sauran fuskantar wannan matsala. “Yadda kuka ga an kawo wannan tallafin abin da Allah ya hore mana, haka muka kai irinsa a sauran Kananan Hukumomin da wannan iftila’i ya shafa”.
Shi kuwa Sarkin Ruman, bayan ya yi jinjina da godiya ga wannan tallafi ya kara yin kira da a ci gaba da yin addu’o’in samun zaman lafiya a kasa baki daya.