Gidauniyar Ibadur Rahman ta koya wa matan aure sana’o’i a Ibadan
Shugaban Gidauniyar Ibadur Rahman da ke Sabo Ibadan, Ustaz Salisu Lukman Mai Borno ya yi kira ga matan aure su tashi tsaye wajen koyon sana’o’i da za su taimaka wa maza da ’ya’yansu wajen gudanar da kyakkyawar rayuwa kamar yadda Addinin Mmusulunci ya tanada. Malamin ya yi wannan kira ne a ranar Lahadi a wajen […]
Shugaban Gidauniyar Ibadur Rahman da ke Sabo Ibadan, Ustaz Salisu Lukman Mai Borno ya yi kira ga matan aure su tashi tsaye wajen koyon sana’o’i da za su taimaka wa maza da ’ya’yansu wajen gudanar da kyakkyawar rayuwa kamar yadda Addinin Mmusulunci ya tanada.
Malamin ya yi wannan kira ne a ranar Lahadi a wajen bikin mika takardun shaida ga matan aure 63 da gidauniyar ta dauki nauyin koya musu yadda ake yin sabulun wanka da wanki da man shafawa da man gyaran gashi da jakunkuna.
“Tasirin wannan yana da muhimmanci musamman ta fannin ilimantar da matan aure sanin addininsu da aikin yi da zai bunkasa rayuwarsu da zamantakewa da mazansu,” inji Ustaz Salisu Mai Borno.
Ya ce, dalibai fiye da 500 na Makarantar Markazut Ta’alimil Islamiy da ke koyar da mata zalla su ne suka dauki nauyin kafa wannan sabuwar gidauniya ta Ibadur Rahman Charity Foundation domin tallafa wa kawunansu da sauran mabukata a Unguwar Sabo, Ibadan.
Shugaban Kungiyar Izala ta Jihar Oyo, Alhaji Salisu Abdullahi ne ya shugabanci taron mika takardun shaidar ga daliban wanda aka yi a harabar Masallacin Darud Da’awah dake Unguwar Sabo, Ibadan.
Daga bisani Babban Limamin Masallacin, Ustaz Sani Haruna ya jagoranci baje kolin kayayyakin da matan suka sarrafa.
Da yake kaddamar da gidauniyar Shugaban Izala reshen Unguwar Sabo, Malam Dauda Muhammed ya bayar da gudunmawar Naira dubu 50 a matsayin jarin da zai karfafa gwiwar daliban wajen bunkasa sana’o’in da aka koya musu. Ya yi kira ga jama’a su yi watsi da kayan da ake shigowa da su daga kasashen duniya su rungumi kayan da ake sarrafawa a Najeriya domin bunkasar tattalin arzikin kasa.
Shi kuwa Sardaunan Ibadan, Alhaji Kabiru Hussaini bayan mika Naira dubu 50 a matsayin gudunmawa ya yi kira ga jama’a masu hali su tashi tsaye wajen tallafa wa gidauniyar da kudi da kayan bukatu domin ta kai ga cimma buri.