Gidauniyar Inuwa Garba ta ba dalibai 45 tallafin karo ilimi
Gidauniyar Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Gombe Alhaji Inuwa Garba, ta ba dalibai ’yan asalin jihar tallafin karo ilimi a ranar Lititin da gabata.A lokacin bayar da tallafin ga daliban a dakin taro na majalisar Alhaji Inuwa Garba, ya ce dalilinsa na ba daliban tallafi shi ne ya kula akwai ’ya’yan talakawa marasa karfi da […]

Gidauniyar Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Gombe Alhaji Inuwa Garba, ta ba dalibai ’yan asalin jihar tallafin karo ilimi a ranar Lititin da gabata.
A lokacin bayar da tallafin ga daliban a dakin taro na majalisar Alhaji Inuwa Garba, ya ce dalilinsa na ba daliban tallafi shi ne ya kula akwai ’ya’yan talakawa marasa karfi da yawa da suke fadi-tashin neman ilimi amma ba su da hali.
Shugaban ya ce ya fara tunanin kafa gidauniyar ce tun lokacin da ya halarci wani taro da ’yan asalin Yamaltu Deba suka gudanar don tunawa da marigayi tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji dahiru Mohammed Deba.
Ya ce dalibai 25 aka zakulo daga sassan da yake wakilta watoYamaltu Deba, wadanda da ma da su zai fara, amma sai ya yi tunanin yana da abokan aiki na kwarai a majalisa shi ne ya ba su dama kowannensu ya kawo mutum daya don ya taimaka, hakan ya sa suka zama 45.
Alhaji Inuwa Garba, ya ce taimaka wa harkar ilimi ba na gwamnati ne ita kadai ba, dole sai masu hannu da shuni sun ba da tasu gudumawar.
Tallafin na kudi kowane dalibi zai samu Naira dubu 25 a shekara na tsawon shekara hudu da zai yi a jami’a wanda idan aka hada zai samu Naira dubu 100.
Daga nan sai ya yi kira ga kungiyar ASUU ta yi wa Allah ta janye yajin aikin da take yi don dalibai su ci gaba da karatu.
Wani dan majalisa mai wakiltar mazabar Dukku ta Kudu daga Jam’iyyar APC Alhaji Umar Aminu, ya ce shi ma zai sa tasa gudumawar inda ya cike kudin suka zama Naira dubu 30 ga kowane dalibi.
Da yake jawabin godiya a madadin daliban da suka ci moriyar gidauniyar Yusuf Muhammad Zarma, daga garin Lano, gode wa shugaban majalisar ya yi tare da Umar Aminu bisa tallafa musu da suka yi don su samu su zurfafa karatunsu.
Yusuf Zarma, ya ce ya ji dadin samun wannan tallafi sosai domin tun yana dan sakandare Allah Ya yi wa mahaifinsa rasuwa kuma mahaifiyarsa ba ta da karfin biya masa kudin karatu, fadi-tashi yake yi har ya samu ya biya kudin makaranta da kyar.