Gidauniyar marayu ta taimaka wa iyalai 200 a Bauchi
A ranar Lahadin da ta gabata ne iyalai 200 suka amfana da taimakon kayayyakin abinci daga asusun Gidauniyar Taimakon Marayu da Jama’a Marasa Galihu na Babbar Kasuwar garin Bauchi. Shugaban Gidauniyar Ustaz Ibrahim Arab ya bayyana cewa wannan ba shi ne karo na farko da gidauniyar take taimakawa jama’a ba, aiki ne da ta dade […]
A ranar Lahadin da ta gabata ne iyalai 200 suka amfana da taimakon kayayyakin abinci daga asusun Gidauniyar Taimakon Marayu da Jama’a Marasa Galihu na Babbar Kasuwar garin Bauchi.
Shugaban Gidauniyar Ustaz Ibrahim Arab ya bayyana cewa wannan ba shi ne karo na farko da gidauniyar take taimakawa jama’a ba, aiki ne da ta dade tana gudanarwa. Ya ce kayayyakin a raba su ne domin rage wa jama’a wasu wahalhalun yau da kullum musamman ma yanzu da ake cikin watan azumin Ramadan.
Ya ce amma a bana shirin ya takaita ne ga marayu kuma ya samu ci gaba fiye da na bara wanda bai wuce
iyalai 50 ne suka amfana da shi ba. Kayayyakin da aka raba sun hada da abinci da tufafi da kuma kudi. Kuma kowane gida ya samu taimakonsa ne gwargwadon yawan marayun da ke cikinsa.
Shugaban ya ce sun tattaro sunayen marayun ne da taimakon masu unguwanni yankin, inda daga nan aka tantance su duka saboda gane hakikanin wadanda suka dace da tallafin. A karshe ya yi alkawarin fadada wannan shirin tallafin zuwa sauran kasuwannin da ke cikin gari da kauyukan jihar Bauchi.