Gidauniyar Musa Halilu Ahmed ta raba wa matan aure da matasa 250 tallafi

Gidauniyar Musa Halilu Ahmed ta raba wa matan aure da matasa 250 tallafin Naira dubu goma-goma domin dogaro da kansu a Jihar Kaduna. Shugaban Gidauniyar Alhaji Musa Halilu Ahmed ya ce sun raba kudin ne da hadin gwiwar Hukumar Samar da Ayyukan yi ta Kasa (NDE). Alhaji Musa Halilu ya bayyana cewa duk da cewa […]

Gidauniyar Musa Halilu Ahmed ta raba wa matan aure da matasa 250 tallafi

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i

Gidauniyar Musa Halilu Ahmed ta raba wa matan aure da matasa 250 tallafin Naira dubu goma-goma domin dogaro da kansu a Jihar Kaduna.

Shugaban Gidauniyar Alhaji Musa Halilu Ahmed ya ce sun raba kudin ne da hadin gwiwar Hukumar Samar da Ayyukan yi ta Kasa (NDE).

Alhaji Musa Halilu ya bayyana cewa duk da cewa shi mutumin Jihar Adamawa ne, dole ne ya taimaka wa marasa galihu da ke Jihar Kaduna domin duk abin da ya zama ya faro ne a Jihar Kaduna.

Ya ce matan auren da matasan masu karamin karfi ne da suke bukatar a taimaka musu domin su samu abin yi don ciyar da iyalansu.

“Ni mutumin Adamawa ne; amma duk abin da na zama a rayuwata, ya faru ne daga Jihar Kaduna. Don haka akwai bukatar in taimaka wa mutanen Jihar Kaduna,” inji shi

Ya yaba wa Darakta Janar na Hukumar NDE kan kokarin da suka yi wajen hada gwiwa da shi domin raba wannan kudi ga masu bukata.

Shugaban Hukumar NDE Alhaji Ladan Argungu, ya yaba wa gidauniyar da shugabanta kan irin kokari da ya yi na taimaka wa marasa galihu cikin jama’a. Ya ce a shirye suke su hada gwiwa da duk wani mutum ko kungiya da ke da niyyar taimaka wa marasa galihu a kasar nan.

Ya yi kira ga masu dukiya su yi koyi da gidauniyar wajen taimaka wa talakawan kasar nan musamman wadanda ke zaune cikinsu.

Ya koka cewa yanzu haka akwai marasa aikin yi sama da miliyan 23 da ke gararamba a fadin kasar nan.