Gidauniyar Noma ta nemi gwamnati ta keɓe Ranar Manoma
Kowa ya san tasirin karrama manoma, abu ne mai kyau.
Gidauniyar Noma ta Kasa, ta koka kan gazawar Gwamnatin Tarayya wajen ware Ranar Manoma ta Najeriya duk da gagarumar gudunmawar da suke bayarwa wajen kyautata rayuwar kasar nan.
Gidauniyar ta ce ta ji mamaki yadda babu wata rana da gwamnati ta ware don bikin tunawa da manoma domin ta ji ta bakinsu, ko ta ba su karramawar da ta kamace su.
- Matsalar rashin zuwan mata makaranta ta fi tsanani a Arewacin Najeriya — UNICEF
- Kotu ta tabbatar wa APC nasarar zaben gwamnan Benuwe
Ko’odinetan Gidauniyar, Dokta Samuel Negedu ne ya bayyana haka, yayin da yake zantawa da manema labarai a Hedikwatar Gidauniyar da ke Abuja a shirye-shiryen bikin baje-kolin amfanin gona na kasa karo na 15 da za a yi daga 20 zuwa 24 Nuwamba mai zuwa.
Ya ce, kasashe da dama suna bikin ranar manoma, inda ya ce ba a makara ba don yin abin da ya dace.
“Har yanzu muna kokarin ganin an samar da ranar. Na yi imani cewa hakan na iya faruwa kuma ’yan jarida za su taimaka don cim ma wannan buri.
“Kowa ya san tasirin karrama manoma, abu ne mai kyau wanda manoman suke hankoron wanzuwarsa nan gaba kadan.
“Ina da yakinin wata rana, hakan zai samu,” in ji shi.
Ya bayar da tabbacin cewa gidauniyar a shirye take ta ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen noma a kasar nan ta fuskar manufofi da shawarwari ga gwamnati mai ci.
Dangane da dalilin da ya sa aka dage gudanar da bikin daga Oktoba zuwa Nuwamba, Dokta Negedu ya ce hakan ya faru ne saboda yanayin damina, inda manoma suka yi asara mai yawa a watan da ya gabata.
“Manoman kuma sun ba da shawarar cewa suna so su halarci kalankuwar bayan sun gama girbe amfaninsu,” in ji shi.
Ya ce a baje-kolin noma na bana, masana za su yi musayar bayanai kan ayyana dokar-tabaci kan abinci da Shugaban Kasa ya yi.
“Manufofinmu biyu ne a nan: na daya shi ne mu kasance cikin yanayi mai kyau wajen samar da yanayin da ’yan Nijeriya za su baje kolin amfanin gona da sauran kayayyakinsu ta hanyar da ta dace a wajen kalankuwar.
“Na biyu, mu tattauna manufofin gwamnati na ci gaban harkokin noma da yadda za a aiwatar da su yadda ya kamata,” in ji shi.
Ya ce, “Taken bikin na bana zai zama nazartar yadda za a tabbatar da shelar ta-bacin da Shugaban Kasa ya yi game da wadata da kasa da abinci.”
Bikin zai tattaro manyan masu ruwa-da-tsaki kamar kungiyoyin manoma da na yaki da yunwa da sauransu.
“Saboda idan ana maganar samar da abinci dole ne wasu daga cikin wadannan kungiyoyi su halarta. Za a dama da su yadda ya kamata tun yayin bude taron da bitar karawa juna sani,” in ji shi.