Gidauniyar Rasuulul Aazam ta taya Shugaba Buhari murna

Gidauniyar Rasuulul Aazam ta mabiya Shi’a ta ce nasarar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya samu a zaben da ya gudana kwanan nan wata alama ce da ke nuna amincewar da jama’a suka yi da irin ayyukan alherin da yake gudanarwa a kasa baki daya. Shugaban Gidauniyar, Sheikh Muhammad Nura Dass ne ya bayyana haka […]

Gidauniyar Rasuulul Aazam ta taya Shugaba Buhari murna
Gidauniyar Rasuulul Aazam ta taya Shugaba Buhari murna

Gidauniyar Rasuulul Aazam ta mabiya Shi’a ta ce nasarar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya samu a zaben da ya gudana kwanan nan wata alama ce da ke nuna amincewar da jama’a suka yi da irin ayyukan alherin da yake gudanarwa a kasa baki daya.

Shugaban Gidauniyar, Sheikh Muhammad Nura Dass ne ya bayyana haka a sakon taya murna da ya aike wa Shugaban Kasar a  makon nan.

Sheikh Nura Dass ya taya Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo murnar nasarar da suka samu.  “A madadin dalibanmu da mabiyanmu da dukan masu bin tafarkin Jaafari muna taya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo murna dangane da nasarar da suka samu a zaben Shugaban Kasa. “Muna addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya sanya a yi sauran zabubbuka masu zuwa cikin kwanciyar hankali da lumana. Muna yaba wa Mai Baiwa Shugaban Kasa, Shawarar kan Harkokin Tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno game da kokarin da yake yi na hada kan kungiyoyin addini don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa baki daya,” inji shi.

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta

Sojoji sun daƙile yunƙurin mayaƙan ISWAP a Borno