Gidauniyar Raya garin Lawanti ta tallafa wa marayu 170
Gidauniyar Raya Garin Lawanti (Lawanti Community Debelopment Foundation) da ke karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe, ta tallafa wa marayu 170 da kayan abinci da tufafi da katifu a garin na Lawanti.Tallafin yana daga cikin manufofin kungiyar na tallafa wa marayu da gajiyayyu domin su gudanar da bukukuwan Sallah cikin walwala.Shugaban kungiyar, Malam Abu Ubaida […]
Gidauniyar Raya Garin Lawanti (Lawanti Community Debelopment Foundation) da ke karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe, ta tallafa wa marayu 170 da kayan abinci da tufafi da katifu a garin na Lawanti.
Tallafin yana daga cikin manufofin kungiyar na tallafa wa marayu da gajiyayyu domin su gudanar da bukukuwan Sallah cikin walwala.
Shugaban kungiyar, Malam Abu Ubaida ya shaida wa wakilinmu cewa sun bullo da wannan shiri ne a kungiyance domin rage marayun zafin rashin iyayen da za su kula da su a irin wannan lokaci na sallah.
Ya ce gidauniyar ta Lawanti tana daukar nauyin karatun marayu daga matakin firamare zuwa sakandare, sai ya yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga masu hannu da shuni da jama’ar garin da sauransu su taimaka wajen daukar nauyin karatun yaran zuwa jami’o’i da manyan kwalejoji.
A jawabin Hakimin Lawanti, Lamido Umar Abdussalam, ya bayyana farin ciki kuma ya gode wa kungiyar bisa tallafin da ta bai wa marayun.
Sai ya yi kira ga ’yan siyasa da masu hannu da shuni wajen su kawo nasu tallafin don taimaka wa marayun.