Gidauniyar Renewed Hope ta tallafa wa magidanta sama da 154,000 a Jigawa

Kwamishinan ya ce tallafin zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziƙin karkara.

Gidauniyar Renewed Hope ta tallafa wa magidanta sama da 154,000 a Jigawa

Aƙalla gidaje 154,412 na marasa galihu aka yi wa rajista domin samun tallafin shirin ‘Renewed Hope Social Security Grant’ a Jihar Jigawa.

Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka na Musamman da Harkokin Jin-ƙai ta jihar, Auwal Dalladi Sankara ne, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai.

Ya ce an fara rabon tallafin ne tun a watan Janairu, kuma yanzu ana gudanar da mataki na biyu na shirin.

A cewarsa, zuwa yanzu gidaje 126,636 daga Ƙananan Hukumomi 27 na jihar sun riga sun karɓi katin biyan kuɗin tallafin.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da rabon katunan ga sauran gidaje 27,776 domin su ma su amfana da shirin.

Sankara, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ƙara kuɗin tallafin daga Naira 10,000 zuwa naira 25,000 a duk wata biyu.

Ya ce duk wanda ya ci gajiyar shirin zai karɓi kuɗin sau uku, wanda jimillarsu za ta kai Naira 75,000.

A cewarsa, an ƙara kuɗin ne domin taimaka wa iyalai wajen samun abinci da kuma inganta rayuwarsu.

Ya kuma ce duk da cewa kuɗin ba su da yawa, amma za su taimaka sosai wajen bunƙasa ƙananan sana’o’i da kasuwanci a cikin al’umma.

“Masu sayar da abinci, masu shayi da sauran ƙananan ’yan kasuwa suna amfana da irin wannan tallafi saboda yana ƙara kuɗin da ke yawo a cikin al’umma,” in ji shi.

Kwamishinan ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, saboda goyon bayan da yake bai wa shirye-shiryen da ke taimaka wa rayuwar jama’a.

Ya ce shirin na Renewed Hope na daga cikin tsare-tsaren gwamnatin Tinubu na rage talauci da bunƙasa tattalin arziƙin karkara.