Gidauniyar Sa Ahmadu Bello ta kai dauki ga ’yan gudun hijirar Yobe
Gidauniyar Tunawa da Tsohon Firimiyan Jihar Arewa Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ta bada tallafin kayan abinci na milyoyin Naira ga ’yan gudun hijirar Jihar Yobe don saukaka musu harkokin rayuwarsu. Da yake bada kayayyakin tallafin ga gwamnatin jihar, Manajan Gidauniyar Dokta Shettima Aji ya ce kayayyakin na abinci da suka hada da buhuna 400 […]
Gidauniyar Tunawa da Tsohon Firimiyan Jihar Arewa Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ta bada tallafin kayan abinci na milyoyin Naira ga ’yan gudun hijirar Jihar Yobe don saukaka musu harkokin rayuwarsu.
Da yake bada kayayyakin tallafin ga gwamnatin jihar, Manajan Gidauniyar Dokta Shettima Aji ya ce kayayyakin na abinci da suka hada da buhuna 400 na garin simobita da jarkokin man girki 100 da katan din magi 100 da katan 100 na madara da kuma turamen zannuwa guda 400 sun kawo su ne domin rarraba wa mutanen da rikicin ’yan Boko Haram ya raba su da muhallinsu.
Dokta Aji ya ce Jihar Yobe na cikin jihohin Arewa da suke da ruwa da tsaki a Gidauniyar Sa Ahmadu Bello. Babban Sakataren Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SERA), Alhaji Musa Idi Jidawa wanda ya karvi tallafin a madadin gwamnatin jihar ya gode wa gidauniyar kan kawo wannan tallafi, inda ya ce an kawo su a daidai lokacin da ake da bukatarsu.
Sai ya bada tabbaci ga mambobin gidauniyar cewa hukumarsu za ta rarraba kayayyakin ga wadanda abin ya shafabisa tsarin da hukumar ke da shi. Sakataren na Hukumar SERA ya gargaddi al’umma musamman mazauna Damaturu su yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa hukumar na bada fom-fom ga jama’a a matsayin shaidar karvar kayan tallafi da wasu vatagari ke sayarwa da sunan hukumar.
Ya ce hukumar tana da tsarinta na rarraba kayayyakin tallafi wanda ya yi hannun riga da hakan.