Gidauniyar Sawaba za ta ci gaba da akidar NEPU da PRP – Balarabe Musa

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya ce wata sabuwar cibiya mai suna ‘Gidauniyar Sawaba’ za ta ci gaba da yadawa da habaka akidar tsofaffin jam’iyyun NEPU da PRP. Alhaji Balarabe Musa ya bayyana haka ne a dakin taro na Gidan Mambayya a Kano ga magoya bayan jam’iyyun na NEPU da PRP. Ya […]

Gidauniyar Sawaba za ta ci gaba da akidar NEPU da PRP – Balarabe Musa
Gidauniyar Sawaba za ta ci gaba da akidar NEPU da PRP – Balarabe Musa

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya ce wata sabuwar cibiya mai suna ‘Gidauniyar Sawaba’ za ta ci gaba da yadawa da habaka akidar tsofaffin jam’iyyun NEPU da PRP.
Alhaji Balarabe Musa ya bayyana haka ne a dakin taro na Gidan Mambayya a Kano ga magoya bayan jam’iyyun na NEPU da PRP.
Ya ce “Don haka muke neman dukan ’yan kasa masu kishi su hadu da mu a daidai wannan lokaci da muke sanar da kafa Gidauniyar Sawaba domin gwagwarmayar farfado da kyawawan ta’adu da akidun NEPU da PRP na samar da kyakyakkyawar rayuwa a karkashin ingantaccen shugabanci mai adalci da tsarin siyasa mai tsabta.”
Ya bayyana takaicin cewa a yau ’ya’yan talakawan da NEPU da PRP suka yi gwagwarmayar kwatar musu ’yanci ne suke tozarta amana da yin mulkin danniya da almubazzaranci da dukiyar kasa.
Malam Balarabe Musa ya ce Gidauniyar Sawaba ba ta gwmanati ba ce kuma ba jam’iyyar siyasa ba ce, illa cibiyar da za ta rika raino da koya wa jama’a kyawawan ta’adu na dimokuradiyya domin gyaran al’amuran siyasa da suka tabarbare.
Ya kara da cewa tabarbarewar harkokin siyasa nd rashin gaskiya da rikon amana da cika alkawari da ke faruwa ne ya damu su tsofaffin ’yan gwagwarmayar kwatar hakkin talakawa a kasar nan suka ga cewa ba za su gajiya ba, sai sun ci gaba da fadakar da jama’a game da kyakkyawar alkiblar da ta kamata su fuskanta.