Gidauniyar Sheikh Niasse ta yi Layya da shanu 200 don raba wa marasa karfi
Gidauniyar Sheikh Niasse ta yi Layya da shanu sama da 200 don tallafa wa marasa karfi 1600 a garin Kazaure da ke Jihar Jigawa. Gidauniyar wadda Musulmin kasashen Ingila da Jamus da kasashe 150 suka kafa tana tallafa wa marasa karfi ne a kasashen duniya. An raba naman Layyar kowace saniya ga mutum 10 a […]

Gidauniyar Sheikh Niasse ta yi Layya da shanu sama da 200 don tallafa wa marasa karfi 1600 a garin Kazaure da ke Jihar Jigawa. Gidauniyar wadda Musulmin kasashen Ingila da Jamus da kasashe 150 suka kafa tana tallafa wa marasa karfi ne a kasashen duniya.
An raba naman Layyar kowace saniya ga mutum 10 a garin na Kazaure. Sai dai a wajen rabon wanda ya samu halartar dubban mutane daga yankin masarautar Kazaure, an ji wa guragu da makafi raunuka, lokacin da aka tattake su garin wawason naman a harabar makarantar firamaren kwana ta Kazaure a ranar Sallar.
Hakan ya biyo bayan sabanin da aka samu tsakanin ’ya’yan gidauniyar da jami’in ’yan sanda mai kula da shiyyar Kazaure da ake kira da Muhammad Fagge, bayan da wata matar Sheikh Muhammad Abdul’ahad Ibrahim Niasse ta ce Fagge ya zo yana yi musu barazana yana tsorata su wai sun shigo Najeriya babu izini alhalin ba aikinsa ba ne ya tambaye su. Ta ce sun ba shi dukan bayanan da ya bukata amma sai da ya nemi ya keta musu mutunci lamarin da ya sa aka daka wa naman da suka yanka wawa.
Ta yi zargin cewa sun ba jami’in leda 20 na naman amma ya bukaci a kara masa da suka ki amincewa sai yake yi musu wannan zagi.
Sai dai da yake bayani a lokacin da suke hayaniya da matar, Fagge ya ce zaginsa ta yi saboda haka ya janye tsaron da ya samar a wajen, sakamakon haka ne mutane suka fada cikin wurin suka daka wa naman wawa.
Da yake karin haske Sheikh Muhammad Niasse dan Sheikh Ibrahim Kaulaha, ya ce ba su ji dadin lamarin day a faru a Kano da Kazaure ba, saboda a Kano wadansu marasa da’a har yankarsa suka yi da wuka lokacin da suka kai naman fadar Mai martaba Sarkin Kano domin raba wa wadanda suka bai wa kati.
Ya ce matasa a Kano sun wawashe nama sama da leda 500, kuma a wurin kokawar ce wani ya yanke shi da wuka, Allah ne Ya kiyaye da ya cire masa yatsun hannu biyu.
Ya ce sun sayo shanun 200 daga kasuwannin yankin kowace a kan Naira dubu 90, duk da wahalar kawo ta. Ya ce a kasashe 360 aka gabatar da irin wannan Layya a duniya, inda a Najeriya ake yin Layyar a jihohin Kano da Jigawa da Katsina. Ya ce a Kano mutum 2,200 suka amfana, a Jigawa mutum 1600, yayin da a Katsina mutum 1,200 suka amfana.
Ya ce saboda rashin tsaro da suke fuskanta a Najeriya in za su sake rabon nama irin wannan za su tuntubi kwamashinonin ’yan sandan jihohi wajen samar da tsaro a duk cibiyar da su gudanar da aikin rabon naman ga mabukata.