Gidauniyar T.Y. danjuma ta gina tare da mika asibitin haihuwa a Taraba
A ranar 19 ga Disamban 2017 ne Gidauniyar T. Y. danjuma ta mika asibitin haihuwa na zamani da gidauniyar ta gina a garin Takum da ke Jihar Taraba. Gidauniyar ta yi haka ne don ta rage aukuwar mutuwar yara da mata masu juna biyu a jihar. Mu’assasi kuma Shugaban Gidauniyar, Janar T. Y. danjuma, yayin […]
A ranar 19 ga Disamban 2017 ne Gidauniyar T. Y. danjuma ta mika asibitin haihuwa na zamani da gidauniyar ta gina a garin Takum da ke Jihar Taraba. Gidauniyar ta yi haka ne don ta rage aukuwar mutuwar yara da mata masu juna biyu a jihar.
Mu’assasi kuma Shugaban Gidauniyar, Janar T. Y. danjuma, yayin kaddamar da Asibitin Haihuwa na Rufkatu danjuma da ke Takum ya ce, ya kadu da rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), wanda ya ce mata 140 da kananan yara ’yan kasa da shekara biyar dubu biyu ne suke mutuwa kullum a Najeriya.
danjuma wanda ya bayyana asibitin na zamani wanda ke cike da kayayyakin kiwon lafiya na zamani da suka dace da kula da lafiyar uwa da danta, ya ce an gina shi ne domin samar da inagantacciyar kula da lafiyar mata masu juna biyu da kula da awonsu ga al’ummar garin Takum da kauyukan da ke kewayensa.
Ya ce aikin hadin gwiwa ne a tsakanin Gidauniyar T.Y. danjuma da Gwamnatin Jihar Taraba da kungiyar Bunkasa Afirka (Debelopment Afrca) wadda ita za ta rika kula da asibitin.
Janar danjuma ya yi kira ga mutanen Takum su yi amfani da asibitin don rigafin mace-macen mata masu juna biyu da kananan yara.
A jawabin, Gwamna Darius Ishaku wanda ya halarci bikin, ya ce asibitin ya nuna “Kulawar da danjuma ke bayarwa ga jin dadin rayuwar jama’a musamman marasa galihu,” inda ya ce, “Gwamnatin Jihar tana alfaharin haduwa da ita a gudanar da wannan gagarumin aiki.’
Gwamna Ishaku ya kuma nemi al’umomin yankin Takum su dauki asibitin a matsayin dukiyarsu da za su “kula da shi cikin kishi” a matsayinsa na babban abin amfani ga al’ummar yankin.