Gidauniyar tallafa wa wadanda hare-haren Boko Haram suka tagayyara yaudara ce – Mustafa Inuwa
Dokta Mustafa Inuwa shi ne shugaban Jam’iyyar APC reshen Jihar Katsina, ya ce gidauniyar tallafa wa wadanda hare-haren kungiyar Boko Haram ta tagayyara da Shugaba Jonathan ya kaddamar salo ne na yaudara: Aminiya: A kwanaki ne Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya kaddamar da wata gidauniya don tallafa wa wadanda hare-haren kungiyar Boko Haram suka […]
Dokta Mustafa Inuwa shi ne shugaban Jam’iyyar APC reshen Jihar Katsina, ya ce gidauniyar tallafa wa wadanda hare-haren kungiyar Boko Haram ta tagayyara da Shugaba Jonathan ya kaddamar salo ne na yaudara:
Aminiya: A kwanaki ne Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya kaddamar da wata gidauniya don tallafa wa wadanda hare-haren kungiyar Boko Haram suka shafa, yaya kuke ganin wannan gidauniya? Dokta Mustafa: Abin da nake gani, mutane sun kasa gane wani salo na yaudara da gwamnatin Jonathan ta Jam’iyyar PDP take yi a Najeriya nan baki daya. Wato saboda kasawarsu ga yin abin da ya kamata, musamman abin da ya shafi harkar tsaro, sai a ga nan-da-nan sun kirkiro wani wanda zai dauke hankalin mutane, bayan kwana biyu ko mako daya ko biyu ko uku sun ga ya kare an sake shiga cikin wani hali sai su sake kirkiro wani. Misali, tunda aka fara abubuwan nan abin da ya damu mutane, a dauki matakai muhimmi domin a samu maganin wannan al’amari. Kuma suka zo suka nemi kudi shekara uku da suka wuce, duk shekara mafi yawan abin da ake ba bangaren tsaro ya fi kowane bangare a kasafin kasar nan. Amma har yanzu halin da ake ciki ba abin da ya canja sai ma karuwa yake yi. An mayar da rayukan mutane kamar rayukan kiyashi, za a je a kashe kamar ma ba a kashe kowa ba. To ka ga ta nan an kasa yin komai don babu tunanin a yi, babu niyyar a yi komai, sai a kirkiro wasu abubuwa, yau a ce taron kasa da an gama sai a kirkiro wani abu da ake ganin zai jawo hayaniya cikin kasa a yi ta surutu kansa. Yanzu misali, saboda Allah da Annabi gwamnatin da ta san abin da take yi ana kashe rayuka ana lalata dukiyar jama’a, ana yin abubuwan da sun hana mutane zaman lafiya, maimakon gwamnati ta fuskanci wannan wai sai a tara taro na mutanen PDP, domin in aka lura kashi 99 cikin 100 na wadanda aka gayyato suka zo wurin kaddamar da gidauniyar ’yan PDP ne ko wadanda suke da alaka da PDP. Wai za su tara kudi domin a je a tallafa wa mutane, wannan abin da suke nema ne, abin da suke jira ke nan? Ina ma maganar zaman lafiyar? Ina wadanda za a tallafa mawa? Tu tuni sun gudu wasu ma sun bar kasar, sun shiga kasashen Nijar da Kamaru, wasu sun tafi Chadi, wasu sauran jihohin. Ina ma za ka gan su a warwatse ka tallafa musu. Kasan wannan ba shi ne ihu bayan hari. A dawo da tsaro da kwanciyar hankali, a dawo da zaman lafiya a wannan yankin shi ne mutane suke nema. Su dawo su ci gaba da karatu da noma da sana’o’insu da suka saba na yau da kullum. Ina tabbatar wa mutane cewa ga yadda aka taho wannan gwamnatin ba ta iya yin wannan, kuma na tabbatar ba ta da bukatar yin su. Kuma idan ka dauki can baya, ai akwai abubuwan da ba su kai wannan muhimmaci ba, gwamnati ta dauki kudi ta bayar. Nan masu Fim din nan Gwamnatin Tarayya ta debo kusan Naira bilyan uku aka ce an ba su domin su inganta abubuwan da suke yi na fim. Nan Gwamnan Jihar Borno ya gaya mana abin da Gwamnatin Tarayya ta ba su gudunmuwa Naira miliyan 150, kuma duk hidimar da ake yi da sojoji a jihohin da suke aikin nan gwamnatocin jihohin ne suke daukar nauyi.
Aminiya: Ka ce mafi yawan masu kaddamar da gidauniyar ’yan PDP ne, amma wadanda aka yi dominsu sun fito daga jam’iyyu daban-daban ne, me ya hana jam’iyyarku ta APC shiga?
Dokta Mustafa: Yo mu za mu kai kanmu mu ce za mu yi, ai wadanda aka gayyata su za su je ko? Saboda haka abin da suka yi ke nan. Wa ma ya sani kila ko harkar tara wa PDP kudin kamfen ne ake ta wata hanya, tunda an ce an kwashi kudin gwamnati ma any i aikin kamfen da su, to ina ga an ce an tara kudin da za a ba marayu da gajiyayyu ne. Saboda haka wani abu an riga an yi. Kuma ina tabbatar maka ba shi ne gaban mutane ba. Kuma ba kwanan nan aka yi wani abin kunyar ba, aka kira mutanen nan suka zo aka ce Shugaban kasar ya ba su Naira miliyan 100, nawa-nawa aka rarraba musu? Ko wannan kudi da aka tara dominsu ina tabbatar maka yadda suka saba kwashe kudin gwamnati haka za su kwashe wadannan. Mutanan da ba Allah suka sani ba, ba kuma tsoronSa suke yi ba, kuma ba jama’a suke tausayi ba. In da jama’ar suke mawa ai gwamnati ce hannunsu, suke da sojoji da ’yan sanda. Yanzu ka duba abin da aka yi wajen zabubbuka. Shugaban kasa da bakinsa ya fadi cewa za su kai dukkan matakan tsaro domin a yi zabe, amma an kasa kai matakan tsaro a jihohin Borno da Yobe da Adamawa da Kaduna. Ka ga wannan abin da gwamnati ta ga dama shi take yi ba abin da yake shi ne jama’a suke da bukatar a yi musu ba.
Fatarmu a nan ita ce Allah Ya ba mu ikon canja wannan gwamnati. Wannan gwamnatin in ba kauda ta aka yi ba a zaben 2015 wadannan abubuwa da ake fama da su, sai dai a ce Allah Ya kiyaye. Ba ka jin yanzu ya ce nan da Disamba, da can yaushe aka ce mana? To ka ga da an shiga Disamba ana maganar zaben da za a yi a watan Fabrairu, saboda haka duk yaudara ce. Ya kamata mu san wannan mu al’ummar wannan bangare, mu abin ya shafa mu yake wahalarwa kuma ake lalata wa tattalin arziki da sauransu.
Aminiya: Wasu daga cikin ’yan adawa na cewa wannan gidauniya tamkar kura ce da kan akuya, me z aka ce?
Dokta Mustafa: Gaskiya ne ni ma na fada. Na daya dai an ce za a tara kudi wa ya san me za a yi da su? A can mun ji labarin yadda aka debi kudin masu fansho wadanda suka shekara 35 suna aiki suka gama, kudinsu aka kwasa aka yi kamfe. Kuma kowa ya ji Dala biliyan 20 ta Amurka ta bace har yanzu ba a maganarta, to ina ganin wannan na taro wannan ya kawo wancan ya kawo, ba ma sai an ga inda aka yi da su ba. Saboda haka wannan ungulu ce da kan zabo. kumbiya-kumbiya ce, kuma babu inda za ta je. Aminiya: Kudin da aka ce an ba iyayen ’yan matan Chibok Naira miliyan 100, gwamnati ta musanta bayar da su, me za k ace?
Dokta Mustafa: Ba gaskiya ba ne, don dai sun ga abin kunya ne, amm sun ba da. To mutanen hauka suke yi da za su ce an ba su Naira dubu 100 ko dubu 200 daga sama suka fado?
Aminiya: To yanzu mene ne mafita ga Arewa?
Dokta Mustafa: Shi ne na ce, mutane su tashi su kori Jam’iyyar PDP a zabe, iyakarta ken an. Su kori gwamnatin PDP duk inda take. Duk wani abu sabanin wannan bata lokacinmu muke yi. Gwamnatin PDP ba ta iyawa, ba ta da niyyar yi. Saboda haka da na jihohi da na tarayya mu tashi tsaye mu yi duk abin da za mu iya yi, mu tabbatar mun samu gajiyar canja gwamnatin nan ta PDP. Ina tabbatar maka in wannan gwamnatin ta sake cin zabe, wasu abubuwan sai dai su zama tarihi.