Gidauniyar tallafa wa wadanda ta’addanci ya shafa

Daga cikin martanin GwamnatainTarayya ga kalubalen hare-haren Boko Haram, akwai yunkuri na bayan nan na sake dawo da wadanda ta’addancin ya shafa cikin hayayyacinsu, wanda babban abin yabo ne. Ba tare da lura da abubuwan da suka faru a baya ba, ta nuna akwai bukatar tausaya wa wadanda ta’addancin ya shafa. Majalisar kasa a karkashin […]

Gidauniyar tallafa wa wadanda ta’addanci ya shafa
Gidauniyar tallafa wa wadanda ta’addanci ya shafa

Daga cikin martanin GwamnatainTarayya ga kalubalen hare-haren Boko Haram, akwai yunkuri na bayan nan na sake dawo da wadanda ta’addancin ya shafa cikin hayayyacinsu, wanda babban abin yabo ne. Ba tare da lura da abubuwan da suka faru a baya ba, ta nuna akwai bukatar tausaya wa wadanda ta’addancin ya shafa. Majalisar kasa a karkashin Shugaba Goodluck Jonatahan ta kafa Gidauniyar Tallafa wa Wadanda Ta’addanci ya shafa da manufar sake tsugunawar da dawo da wadanda hare-haren ta’addancin ya shafa a Arewa maso Gabashin kasar nan cikin hayyacinsu, inda nan ne aka fi kai wa hare-haren.
Domin kula da gidauniyar an kafa wani kwamiti na masu dukiyar Najeriya a karkashin shugabancin hadin gwiwa na Janar Theophilus Yakubu Danjuma, tsohon Ministan Tsaro da kuma Mista Fola Adeola, wani na sahun gaba a a cikin ’yan kasuwar Najeriya.
Shirin Sake Ginin kasa na 1945 da Amurka ta tsara don sake gina Yammacin Turai bayan Yakin Duniya na Biyu ya daidaita ne ya jawo kafa wannan gidauniya wadda za ta fara aiki da Naira biliyan 30, inda Gwamnatin Tarayya za ta bayar da Naira biliyan 10, sannan jihohi 36 za su bayar da wannan adadi, sai kuma ’yan kasuwa su samar da sauran Naira biliyan 10. Sai dai kuma a wajen walimar kaddamar da shirin an tara Naira biliyan 65 sama da abin da aka yi niyya na kudi da alkawari, lamarin da ke nuna kauna da tausayawar da jama’ar Najeriya suke yi ga jama’ar Arewa maso Gabas. Gidauniyar za ta mayar da hankali ne wajen sake gina makarantu da gine-ginen da maharani suka lalata.
Abin lura wannan yunkuri yana zuwa ne a lokacin da ake fama da bala’i a yankunan da lamarin yake shafa, musamman jihohin Borno da Yobe da Adamawa, wadanda suke karkashin dokar ta-baci na tsawon lokaci. A lokutan hare-haren an rika ruguza daukacin garuruwa ana fatattakar mazaunansu suna watsuwa zuwa cikin sassan kasar nan da wajenta a matsayin ’yan gudun hijira, harkokin tattalin arziki sun tsaya cik, sannan an rasa daruruwan rayuka tare da lalata dimbin dukiya. Hatta wuraren ibada kamar coci-coci da masallatai an rugurguza su tare da hallaka masu ibada a cikinsu. Kuma mafi ban takaicin mugun aikin ta’addancin shi ne sace ’yan mata fiye da 200 daga cikin makarantarsu da ke Chibok a Jihar Borno.
Kamar yadda Shugaba Jonathan ya bayyana, ’yan matan ’yan makaranta da sauran dukkan wadanda hare-haren suka shafa barrantattu ne da suke rayuwa irin ta talakawa a lokacin da ’yan ta’addan suka auka musu da barna inda suka rika kashe su da raba su da sassan jikinsu suka raba su da jin dadin rayuwa da dukiyarsu. Wannan ne dalilin da suka cancanci jama’ar daukacin kasar nan ta tausaya musu ta tallafa musu, kamar yadda manufar kafa gidauniyar ya kunsa. Za su iya ci gaba da jin zafin rikicin na wani lokaci, bakin cikinsu ta wata hanya ta daukacin ’ya Najeriya ne, saboda burin maharan shi ne su bata martabar daukacin kasar. Babu dan Najeriya daga kowane bangare na kasar da zai iya ko zai ji a jikinsa cewa ya kubuta daga wannan mugun aiki da maharan ’yan Boko Haram ke yi.
Kuma lura da muhimmancin wannan yunkuri, yana da kyau a tunato da cewa lura da tarihin tallafi ga ire-iren wadannan matsaloli da aka bullo da su a baya akwai bukatar kwamitin da Janar danjuma ke jagoranta ya tabbatar ya sauke nauyin da aka dora masa ta wajen sadaukar da kai da yin aiki wurjanjan don tabbatar tallafin ya isa hannun wadanda lamarin ya shafa. Za a cimma wannan nasara ce idan kwamitin ya bayar da damar kulla dangantaka tsakaninsa da masu ruwa da tsaki da ke shiyyar da suka hada da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi da kungiyoyin ’yan kasuwa da sarakuna da shugabannin al’umma da makamantansu.
Kuma akwai bukatar kwamitin ya mayar da hankali wajen inganta tattalin arzikin wadanda hare-haren suka shafa ya shallake na kafin lokacin Boko Haram. Wannan fatar na nuna irin kalubalen da ke gaban kwamitin. Yana nufin kada gidauniyar ta zama ta raba kudi ga daidaikun mutane wadanda suna iya kashe su ta hanyar da ba ta dace ba – duk da cewa akwai bukatar a magance wasu bukatun gaggawa da bangare ne na aikin kwamitin. Wajibi ne a samar da wani gamammen shiri da zai kawo ingantar tattalin arziki da zai kawo ci gaba mai amfani inda samar da masana’antu zai samu kula ta musamman. Wannan zai canja halin da yankin ke ciki kuma a cimma bukatun daukacin ’yan Najeriya wadanda a zahiri suna haba-haba su ga an kawo karshen wannan bala’i da hare-haren Boko Haram suka jawo wa kasar nan.