Gidauniyar Ufuk ta dau nauyin ciyar da mutum 1000 a yayin buda-baki
Wata gidauniyar ayyukan jinkai, mai suna Ufuk Dialogue Foundation da kungiyar Turkawa mazauna Najeriya ke gudanarwa, ta kaddamar da shirin ciyar da mabukata 1000 a yayin buda-baki da zai rika gudana a Babban Masallacin kasa da ke Abuja. Abinci wanda ke kunshe a cikin kwanon tafi-da-gidanka, za a rika raba shi ne ga mabukata a […]
Wata gidauniyar ayyukan jinkai, mai suna Ufuk Dialogue Foundation da kungiyar Turkawa mazauna Najeriya ke gudanarwa, ta kaddamar da shirin ciyar da mabukata 1000 a yayin buda-baki da zai rika gudana a Babban Masallacin kasa da ke Abuja. Abinci wanda ke kunshe a cikin kwanon tafi-da-gidanka, za a rika raba shi ne ga mabukata a tsawon kwanakin watan azumi. Jami’in yada labarai na kungiyar, Mista Sabas Tuylu a ya shaida wa wakilinmu cewa kungiyarsu ta yanke shawar samar da abincin ne, don rage gibi da ke akwai a tsakanin matalauta da mawadata a fuskar abinci.
Ya ce tsarin wanda kungiyarsu ta fara a bara, na gudana ne a cibiyoyi 14 a garuruwan da makarantunsu na Nigerian Turkish International College suke, kuma suna samun karin tallafin daga wata gidauniya da ke kula da makarantun. Wakilinmu ya ce, mutanen da suka yi cincirindo a wajen raba abincin buda-bakin, sun yi layi kashi biyu na maza da na mata, a yayin da jami’an kungiyar ke mika musu abincin ba tare da wani jidali ba.