Gimbiya Florence Ayi : Mata a shiga siyasa

Gimbiya Florence ‘yar Sarkin Garaku da ke Jihar Nasarawa ce, kuma fitacciyar ’yar siyasa ce, ta ce tana da yakinin mata ne za su iya ceto kasar nan daga halin da ta fada, shi ya sa ta bukaci mata su shiga siyasa a dama da su. Daga John D. Wada, a Lafiya Tarihin RayuwataSunana Gimbiya […]

Gimbiya Florence Ayi : Mata a shiga siyasa

Gimbiya Florence ‘yar Sarkin Garaku da ke Jihar Nasarawa ce, kuma fitacciyar ’yar siyasa ce, ta ce tana da yakinin mata ne za su iya ceto kasar nan daga halin da ta fada, shi ya sa ta bukaci mata su shiga siyasa a dama da su.

Daga John D. Wada, a Lafiya

Tarihin Rayuwata
Sunana Gimbiya Florence Ayi, ni ce Gimbiyar Toti. Ni kabilar Gwandara ce daga Garaku Hedikwatar karamar Hukumar Kokona a Jihar Nasarawa. Kuma mahaifina shi ne Sarkin Garaku, wato mai martaba Dokta Silbester Ayi. Bayan na kammala karatuna sai na yi aiki da Hukumar Samar da Kudin Shiga ta Jihar Nasarawa, daga bisani na shiga harkar siyasa inda na fara da jam’iyyar PDP. Ban jima a jam’iyyar ba don na lura cewa ba jam’iyyar da zan iya ci gaba da tafiya da ita ba ne, saboda ta kasa ceto talakawan kasar nan daga halin kunci da suke ciki. Daga nan na canja sheka zuwa jam’iyyar CPC, wadda yanzu ta narke zuwa APC. A yanzu dai ni cikakkiyar ‘yar jam’iyyar APC ce gaba da baya. Kuma ina rike da mukamin ma’ajin kudin Jam’iyyar APC ta jihar nan.
Halayen da na koya a wurin iyayena
Ni dai har yanzu ina tare da iyayena. Domin babu makon da zai wuce ba tare da na je gidan iyayena ba. Kowace Juma’a nakan je garinmu Garaku in gaishe da iyayena, sai dai idan wani uzuri ya sha kaina; nakan je Juma’a na dawo Lahadi ko Litinin da safe. Mahaifina sarki ne, kuma tsohon malami ne wanda ke daya daga cikin wadanda suka kafa makarantar ATC da ke karamar Hukumar Akwanga a Jihar Nasarawa. Ba mai son magana ba ne sosai. Kamili ne mai son gaskiya da rikon amana a kodayaushe. Idan zai iya yi maka wani abu, to zai yi maka, idan kuma ba zai iya ba zai gaya maka. Yana da hakuri sosai, don wasu mutane sukan yi amfani da damar hakurinsa su taka masa hakkinsa. Amma duk hakan ba ya nuna damuwa. Wadannan halaye ya koya mana. Babban abin da ya koya mana shi ne yafiya. Yana so ‘ya’yansa su zama masu yafiya. Hakan ya sa babu wani laifi da mutum zai yi mini a nan duniya da ba zan iya yafe masa ba.
Nasarori
A tawa fahimtar nasara ita ce, idan mutum ya cim ma burinsa a rayuwa komai kankantarsa. Misali,  idan kana so ka gina gida, za ka fara idan har Allah Ya sa ka gama, to ka cim ma nasara ke nan a wannan bangaren. Ni dai da yardar Allah na cim ma nasarori da dama a rayuwata, domin ta kasance mini kamar yadda nake so. Na samu nasarori a wurin aikina. Haka ma a bangaren siyasa ina gaba- gaba, wanda hakan ya sa aka ba ni mukamin ma’ajin kudin jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa, kuma ina ci gaba da ba da gudunmawata a kullum don ci gaban jam’iyyarmu.
Ga bangaren kungiyoyin mata da muka kafa ma muna taimakawa. Saboda haka a takaice dai na samu nasarori da dama. Ina yi wa Allah godiya kan wadannan nasarorin.

kalubale
A rayuwa dole ne mutum ya fuskanci kalubale. Amma idan mutum mai sakaci ne sai ya zama masa babban kalubale. Amma idan ya nace ya tunkare shi, sai ya shawo kansa. kalubalen da nake fuskanta yanzu shi ne a bangaren siyasa. Wato yadda za ka ga wasu mutane ke munafurtar junansu, maimakon su rika nuna so da kauna a tsakaninsu. Shi ya sa a kodayaushe a matsayina ta daya daga cikin shugabanni, nakan ja hankalin jama’a don su fahimci muhimmancin zaman lafiya da nuna so da kauna ga junansu. Hakan kuwa sai ya kasance mini babban kalubale.  Ina so jama’a su koyi zaman lafiya da son junansu don a samu ci gaba mai dorewa.
Abin da nake so a tuna ni da shi
Ba wai kawai ina so a tuna da ni ta hanyar dariyata da murmushina ba. Babban abin da zan so a tuna da ni idan ba na nan shi ne, irin kyakkyawar mu’amala da kuma cudanyar da na yi da jama’a. A yanzu babu lokacin da za ka zo gidana ba ka ga ina tare da jama’a ba. Kuma mutum ba zai zo gidana bai ci abinci ko ya sha ruwa ba. Saboda haka na tabbata idan jama’a suka zo gidana ba na nan babu abinci ko ruwan sha, ka ga dole ne su tuna da ni.
Shawarata ga mata
Shawarata ga ‘yan uwana mata da ma jama’a baki daya ita ce, kowa ya tashi ya tabbatar da zaman lafiya a duk inda yake. Kamar yadda ka sani kasarmu yau ta zama abin da ta zama. Mata mu rika yi wa ’ya’yanmu gargadi musamman game da illar da ke tattare da fitina. Bayan wannan mata a kama sana’a. Ya kasance mutane sun san ki da sana’a mai kyau. Kada a san ki da mummunan hali don ba zai taimaka wa rayuwarki ba.
A karshe kuma mata a yi kokari a shiga harkar siyasa don a halin yanzu muna fuskantar karancin mata ’yan siyasa a kasar nan baki daya. Ka ga hakan ba alheri ba ne a gare mu ba. Kodayake ba laifinmu mata ba ne, sau da yawa maza ba su ba mu dama ba ne, amma yana da kyau mu nace mu shiga a yi da mu, don mu ne kawai za mu iya tabbatar da shugabanci nagari a kasarmu Najeriya. Mata su fito su kada kuri’u, su kuma tsaya takara don mu kwaci ’yancinmu da sauransu.