Gimbiyar Dubai: Mahaifina ya yi garkuwa da ni tsawon shekaru
Ta shekara biyu a tsare bayan da mahaifinta ya sa aka ‘sace’ ta
’Yar Sheikh Mohammed bin Rashid al Maktoum, Mataimakin Shugaban Kasa kuma Firaministan Hadaddiyar Daular Larabawa, Gimbiya Latifa ta ce mahaifin nata ya yi garkuwa da ita.
A shekarar 2018 Gimbiya Latifa ta yi yunkurin tserewa daga kasar amma jami’an tsaro sun dakile yunkurin nata.
- Yadda ake sayen burodi, haka muke sayen makamai —Daudawa
- Fizgen jaka: Kotu ta ba da belin matashi N500,000
- Sojoji 6 sun rasu bayan Boko Haram ta tarwatsa su ta kwashi makamai
- Sunayen dalibai da malaman da aka sace a Makarantar Kagara
A wasu bidiyon da ta dauka a sace daga inda take tsare tun bayan da aka kama ta a 2018, Gimbiya Latifa ta yi zargin cewa tun lokacin da aka sace ta din take tsare “ba tare da shari’a ko tuhuma ko wani abu ba.”
A bidiyon da shirin BBC Panorama ya samu cewa, “Abin ya kai makura na gaji da komai. Abun ya ki karewa… Ni ’yanci kawai nake so in samu.
“Ban san me suka shirya za su yi da ni ba, kullum abin sai kara ta’azzara yake yi.”
Sai dai kuma bullar sabon bidiyon ya kawo ce-ce-ku-ce a duniya, inda kungiyoyin kare hakkin dan Adam ke ta kira da a bincika lamarin.
A baya dai Dubai da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa sun bayyana cewa ’yar Firaministan na cikin aminci cikin kulawar iyali.
Kafin kama Gimbiya Latifa
Gabanin dakile yunkurinta na tserewa a 2018, Gimbiyar ta saki wani bidiyo a YouTube wanda a ciki ta bayyana abin da take zargin zai same ta a lokacin.
“Masu kallon wannan bidiyon, wani abu mara dadi na dab da faruwa, ko dai na mutu ko kuma in shiga cikin mawuyacin hali,” inji Latifa.
Bidiyonta na 2019
A wani bidiyonta da aka samu a 2019, ’yar ta Sheikh Mohammed bin Rashid al Maktoum, ta ce ana tsare da ita ne a “wani katafaren gida da aka mayar shi gidan yari.
“An toshe duk tagogin, an sa ’yan sanda maza biyar a waje da mata ’yan sanda biyu a cikin gidan, sannan ko tsakar gidan ba a bari in fita,” inji ta.