Gimbiyar Kano za ta auri Basaraken Yarbawa
Za a daura auren Gimbiya Firdauz, jika ga marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero da angonta a ranar 19 ga Maris, 2022
Basaraken kasar Iwo, Adewale Akanbi (Telu I) ya shirya auren ’ya ga Sarkin Kano, Gimbiya Firdauz Abdullahi.
A ranar 19 ga watan Maris 2022 za a za a daura auren Sarkin dag Gimbiyar, wadda ’ya ce ga Sarkin Kano, a gidan Madakin Kano da ke birnin Kano.
- Yadda aka cafke ’yan bindiga 10 a dajin Kwara
- Kotu ta ce ba wanda ya tursasa Abdulmalik Tanko ya ce shi ya kashe Hanifa
An shirya gudanar da walima ta mata zalla a Gidan Rumfa da ke Masarautar Kano a lokacin bikinna Gimbiya Firdauz da Oba Adewale Akanbi.
Tuni shirye-shiryen bikin suka yi nisa tsakanin Gimbiya Firdauz, wadda jika ce ga marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, da masoyin nata.
Gimbiya Firdauz mai shekara ’ya ce ga Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, wato ’yar dan uwansa.
Basaraken wanda ya rabu matarsa ’yar asalin kasar Jamaika a 2019, ya sake samun masoyiya a zuri’ar Bayero da ke Kanon Dabo.