Gina Madatsar ruwa a mazabata za ta kawo karshen yawon ciranin matasa – danmajalisa Gausu
dan majalissar tarayya mai wakiltar karamar Hukumar Ringim da Taura a Jihar Jigawa, Malam Gausu Muhammed Boyi, ya nuna damuwarsa game da yadda ambaliyar ruwan kogin Ringim take azabtar da manoman yankin a duk shekara a lokacin damina lamarin, inda yake haifar da asarar amfanin gona da gidaje, wani lokacin ma har da rayukan jama’a. […]
dan majalissar tarayya mai wakiltar karamar Hukumar Ringim da Taura a Jihar Jigawa, Malam Gausu Muhammed Boyi, ya nuna damuwarsa game da yadda ambaliyar ruwan kogin Ringim take azabtar da manoman yankin a duk shekara a lokacin damina lamarin, inda yake haifar da asarar amfanin gona da gidaje, wani lokacin ma har da rayukan jama’a.
Malam Gausu ya yi wannan korafi ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Dutse, bayan da ya kai wa kwamashinan yada labarai na Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim Mamsa ziyarar girmamawa a ofishinsa.
Gausu ya bukaci gwamnatin tarayya da ta samar da madatsar ruwa a yankin, tsakanin karamar Hukumar Ringim zuwa Garki, domin amfanin manoman yankin. Ya ce samar da madatsar ruwan za ta taimaka wajen magance yawan ciranin matasa zuwa wasu sassa na kasar nan. Kuma zai kawo karshen zaman banza a tsakanin matasan da yake wakilta da ma wadanda ba ’yan mazabarsa ba.
Ya kara a cewar da ma can tun kafin suzama ’yan majalissa akwai waccan bukata ta neman yin madatsar ruwan da daya daga cikin ministocin Buhari ya rubuta tun kafin ma ya san zai zama minister ba. Saboda haka yanzu lokaci yayi da yakamata ya taimaka yatunawa janar buhari danganin anyi wannan dam yakuma bukaci gwamnati tarayya data samarda kogin dole daga ringim zuwa Babura yabita garki yin hakan zaitaimaka wajan magance yawaitar ambaliyar koguna ayankin alokacin damina kuma zaitaimaka wajan samawa matasa aikin yi ya kara da cewar muddin aka yi madatsar ruwan dole a yankin matasa za su samu damar dogaro da kansu maimakon aikin gwamnati.
A cewarsa, akwai wasu kauyuka a lokacin damina duk shekara suna fuskantar barazana a yankin Ringim da Taura, saboda rashin gada domin zirga-zirga tana takaita tsakanin mazauna yankin da karamar hukumarsu, saboda in mutun bai iya ruwa ba, sai an yi masa fito da jirgin ruwa, lamarin da ya sa aka sha samun mutuwar mata masu ciki a daidai lokacin da ake kokarin hayewa da su kogi jirgi ya kife da su.
Yakuma bukaci gwamnatin tarayya da ta taimaka wajen yanke ciyawa kacala da ta toshe magudanan ruwan kogin da ya tashi daga Dabi zuwa iyakarsa da kogin Hadeja, domin toshewar idanun kogin da ciyawar ta yi shi ne yake haifar da ambaliya a kowace shekara.