Gina madatsun ruwa zai taimaka wa manoman Najeriya – Gadzama
Babban Daraktan kungiyar Bunkasa Harkokin Noma ta Green Planet da ke Jos, Mista Paul Gadzama ya ce babban abin da zai taimaka wa manoman Najerya don fuskantar matsalar karancin ruwan sama shi ne a giggina madatsun ruwa a kasar nan. Mista Paul Gadzama ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu kan […]

Babban Daraktan kungiyar Bunkasa Harkokin Noma ta Green Planet da ke Jos, Mista Paul Gadzama ya ce babban abin da zai taimaka wa manoman Najerya don fuskantar matsalar karancin ruwan sama shi ne a giggina madatsun ruwa a kasar nan.
Mista Paul Gadzama ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu kan hasashen Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NIMET) ta yi cewa za a samu karancin ruwan sama a daminar bana.
Ya ce bai kamata manoman Najerya su rika dogara da ruwan sama ba, domin ruwan sama wata rana zai yi yawa wata rana kuma zai kasa.
Daraktan ya ce duk kasashen da suka ci gaba suna amfani da madatsun ruwa ne wajen yin noma. “A kullum ana maganar gina madatsun ruwa a kasar nan amma har yanzu babu wani ci gaba da aka samu kan wannan al’amari.Kuma matukar ba a rungumi gina madatsun ruwa ba, ba za a bunkasar harkokin noma ba,” inji shi.
Ya ce kamar madatsar ruwa ta Tiga da marigayi Gwamna Abdu Bako ya gina, tana ba da gagarumar gudunmawa wajen bunkasa noman rani a Jihar Kano.
Gadzama ya ce amma abin takaici ba a magana kan irin gudunmawar da wannan madatsar ruwa ta Tiga ta bayar a kafofin watsa labarai na kasar nan.
Ya ce za a iya noma masara da gero sau biyu zuwa uku a shekara ta amfani da madatsun ruwan da aka giggina.
Da ya juya kan kungiyarsu ta Green Planet kuwa Mista Paul Gadzama ya ce suna kokarin inganta takin gargajiya da suke yi, ta hanyar amfani da ciyayi da ’ya’yan itatuwa.
Ya ce a bana za mu yada wannan taki zuwa kasuwannin jihohin Filato da Kano da Gombe da Bauchi da Kaduna da sauransu.