Gingimemiyar ganuwar gane gungun gagararru (1)

Gungun gagararru Gangaren gaftarar gutsirar garu Fankamar fandararru Fantsamar fitsararru Karfa-karfan kadangaru   Sasarin sunkuru Samamen sakarkaru Sagaraftu sururu Shammatar shanu shiru Shisshigin shegantakar shekarun shahararru   Zirin zungurar zunguru Zankaleliyar zangarniya zururu Zaman-takewar zuru Zalamar zakwadin zakaru Jama’ar jamhuriyar jimamin  jamhuru   Birane da kayuka Batagari na ta tufka Turmutsitsin jama’a ba masaka An […]

Gingimemiyar ganuwar gane gungun gagararru (1)

Gungun gagararru

Gangaren gaftarar gutsirar garu

Fankamar fandararru

Fantsamar fitsararru

Karfa-karfan kadangaru

 

Sasarin sunkuru

Samamen sakarkaru

Sagaraftu sururu

Shammatar shanu shiru

Shisshigin shegantakar shekarun shahararru

 

Zirin zungurar zunguru

Zankaleliyar zangarniya zururu

Zaman-takewar zuru

Zalamar zakwadin zakaru

Jama’ar jamhuriyar jimamin  jamhuru

 

Birane da kayuka

Batagari na ta tufka

Turmutsitsin jama’a ba masaka

An dai samu baraka

Ba wanda zai kishin kasarka

 

An dai bar kwafa

Wanzami bai son jarfa

Shagabannin sun sha’afa

Duwarwatsu suna ta jifa

Kudundunen hangame hancin shakar kirfa

 

Wasu na ta tsirfa

Matsala tun tana kan akaifa

Aka ki sa ruwa kura ta lafa

Mayafin musifu aka yafa

Har kowa ya fara takewa da kafa

 

Mun samu kanmu a kungurmin daji

Kowa na ta bangaji

Al’umma ta gaji

Kowa so yake akawo agaji

An dai fasko ramin maciji

 

Mafakar muggan magabta

Maboyar munafukai macuta

Makirai mabarnata

Mattatarar masu mugunta

Musun make-maken matalauta

 

Ruruta wutar rudani

Aika-aikar arangamar addini

Ana ta yawan zubar da jini

Sukar balatin kahon hauni

An bar jama’a cike da alhini

 

Zogin zaman zamani

Ga shi ana ta wuni-wuni

Bulkarar bambamin birni

Tsakatsakin tsinin tsanani

Tsoro tsororuwar tsauni

 

Zaman dirshan

Ai ta kishin-kishin

An haifar da asara da gangan

Miyagu sun tunkaro gadan-gadan

Sui sunkurun shan kan

 

Dannin danniya

Dangar dumuiniya

Juwa-juwar juriya

Kakarar karkarar karafkiya

Karyar karan kariya

 

Kayar kauyen kayau

Taga-tagar targade tarau

Karar karajin kure karyar karau

Motsin matso miyau

Gamon gajiyawar gajiyau

 

Rai kwakwai

Mutu kwakwai

Gunyar fashin kwai

Kusan komai da akwai

Al’amura ne bambarakwai

 

Jahilcin jahilai

Dolancin dolaye

Wautar wawancin wawaye

Ana ta abubuwa da maimai

Makomar masanan malamai

 

Mu sake dabara

Mu laluba mu gyara

Mu toshe kafar algarara

Mu yunkura

Mu hanzarta ka da a makara

 

Da tsohuwar zuma ake magani

Dadaddun ta’adu ake gani

Malumma masu sani

Kowa-da-kowa yai matsuguni

Al’umma a kyautata mazauni

 

Kawanyar kewaye-kewaye

Ta’adar gadon ’ya’ya da iyaye

Zamunnan  farmakin mamaye

Katafariyar Katanga ce zagaye

Baraden fada na bi da bibiye

 

Tsarin tsaro

Tsare tsoro

Tururuwar taro

Tunkahon torokon toro

Tsiri-tsirin tsakanin tsiro

 

Gine-ginen ganuwa

Garuruwa na da garkuwa

Bako da bakuwa

Sai sun samu isuwa

Tada kan adda bai bazuwa

 

Zaman zumun zumunta

Mutuncin mutane masu mutunta

Baraden barden bajinta

Carar carkin cakwaikwaiwar cancanta

Dangar duga-dugin dattakun danganta

 

 

Cudeni in cudeka

Dagar dangin dinke baraka

Ba karya doka

Ba duka

Ballantana a koka

 

Kowace mashiga an mata kyaure

Masu shiga a ware

Miyagu a tare

Al’ummar da ba bare

Ko da bakon Baddakare

 

Da zuwan Bature

Kofofi aka sare

Ba wanda za a tare

Tun da an daina hare-hare

Dakarun sarauniya sun kare

 

Bayan ’yancin kai

Tattakin tumakan tunburkai

Da  takun awakai

Ya haifar da sananin son kai

Aka karke  da tutsun jakkai

 

Gantalin gari-gari

Giringidimin gigigiwa giriri

Ga garari

Watangaririya wuri-wuri

Banga-bangar bidirin biri

 

An san mai mukami

ko barden makami

da bakon wanzami

lamura na da masomi

don haka ba jimami

 

Babban mutum mai rawani

Da taimakon malami masani

Yake kula da birni

Duk ba wani bini-bini

Zamunnan iyaye da kakanni

 

Yau

A kwai kayoyi kayau-kayau

Ba bambacin muni da kyau

Magabtan mamugunta kyau-kyau

Dawurwurin dumuiniya darandakau

 

Rayuka bararraje

Al’amura a baje

Ana ta na jan-je

Samarin-kusu na bangaje-bangaje

Kurmusun ciki da waje

 

Talalar talaucin talaka

Wajijjigar wajigawar waraka

Langabun laftun laka

Runtsin raraka

Tsallen tsulan tsallaken tsukukun tsaka

 

Mu bi kadin ta’adar magabata

Mu yaukaka zumunta

Masu mulki a daina karanta

Mutane gari mu zam masu fahimta

Mu rungumi kyawawan ta’adu mu kwatanta

 

Cikinmu a samu zarata

Bin doka a aikata

Halaliya a halatta

Haramiya a haramta

Miyagu a hukunta

 

Tonon sililin wirkilili

Wulkitawar wawan wulli

Komai na da tushen asali

Dukiya da rayuka ba fatali

Sananne ne mai kansakali

 

Haurobiyawa

Garkuwar gagara kuwwa

Tsarin tsaron tsuwwa

Bar bilinbituwa

Ko kai-kawon kokowa

 

Gangar gurmin gunjin gangi

Gungunin gabagadin gigi

Mamungar majigin magagi

Juye-juyen jirkita jirgi

Karkarin kugin kawata kirgi

 

Dar-dar din dari-darin dirkaniya

Doridasonon doriya

Dauke-dauken dakin daukakkiya

Dokin dauko diya

Damarar daukar dawainiya

 

A kiyayi shaci-fadi

Wannan shi ag gargadi

Mu yasar da rudi

Mai toshe ganai da barbadi

Da jin dundumin rade-radi

 

Mugun macucin Tarba-tarba

Yayimar Magajin gari ai awon gaba

Huta-roro yai jibgin jibar jajiba

Satar mutane ya saba

Jihar Tumbin-giwa a kai gaba-da-gaba

 

Birnin Dabo

Ba a dabo

Musifu ne aka jajibo

Ruwan dafa kai aka debo

Kyawawan ta’adu a lalubo

 

Barankadamar Bararon-nono

Bobon bangajen bokokon bonono

Biranen burbudin baza barkono

Babbar magana dai sai da aka auno

Babban bogajin kwano

 

Dakin karar dakon dako

Bin kadin birnin Dikko

Basajen bokoko

Bankaurar hana kwankwadar koko

Laftun lafkewar lakar loko

 

Birnin lawurje

Babu bangaje-bangaje

Bilinbituwar barbaje

Burgujejen buje

Batun nadi da lauje

 

Masu martaba

Masu gidajen yaben makuba

Mutanenku na fama da ukuba

Mahangar mafita za a duba

Malumma a tama wa shugaba

 

Ai kokarin kawar da daba

Masu fuka-fukin tashi ’yan daba

Tarairaya da biyayya ’ya’yan Abba

A kiyayi gaba da giba

Sai al’umma tai galaba

 

Ina Magajin gari

Babban attajiri

Alaramma uban almajiri

A kula da uwar jinjiri

A kyauta karatun kumsar kuri

 

A daina kasala

A yaki juhala

A tabbatar da adala

A samu sa’idar lalala

Kowa ya samu walwala

 

Baraden burka bindiga

Ba bugi-in-buga

Ku ja tunga

Da dogewar daga

Ku ne gaggan gwanayen sabga

 

Jami’an asiri

A kara himmar kokari

Kui kundin bayanan sirri

Ban da jinkiri

Lallai ku zama masu jimiri

 

Sai birane sui kasurar kasaita

Karkara ta kambama a tarairayeta

Mazaunan unguwanni su kubuta

Daga zullumin zaman ragaita

’Yar burum-burum ai da zarata

 

Ginin gingimemiya

Ganuwar ganin giginya

Gane-ganen gogoriyon ganiya

Garambar gantalin Gambiya

Gungun gagararrun gangariya

 

Can a kasashen duniya

An yi bajintar nuniya

Da kwazon hana danniya

Mutane sun rage tankiya

Rabautar ribar romon ragon Romaniya

 

Binciki Barbados

Bar batun Bahamas

Ban san me a kai a Beralus

Ba bangon Berlin a Jamus

Bi-da-bin kalmomin kamus

 

A zo a bi doka

A bar zaluncin duka

Macuta a kama

Su gurfana gaban hukuma

Har a sha kan kiki-kaka

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos