Gini mai hawa 3 ya rufta kan mutane a Legas

NEMA ta ce ba ta san adadin mutanen da ginin ya danne ba.

Gini mai hawa 3 ya rufta kan mutane a Legas

Wani gini mai hawa uku da ake ginawa ya rufta kan mutane a unguwar Yaba, da ke Jihar Legas.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta ce ginin ya rufta ne da misalin ƙarfe 8 na dare.

Shaidu sun ce akwai mutane biyar zuwa shida a cikin ginin lokacin da abin ya faru.

NEMA ta ce ta ceto mutum huɗu, kuma an garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu.

Sai dai hukumar ta ce ba a tabbatar da adadin waɗanda har yanzu suke ƙarƙashin ginin ba, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.