Gini ya kashe mutum 7 a sansanin ’yan gudun hijira a Borno

Tuni aka yi jana’izar mutanen ranar Talata

Gini ya kashe mutum 7 a sansanin ’yan gudun hijira a Borno

Wasu ‘yan gudun hijirar Najeriya

Akalla mutum bakwai sun rasu, wasu biyu sun jikkata bayan wani gini ya rushe a sansanin ’yan gudun hijira da ke Monguno a Jihar Borno.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) ya rawaito cewa ginin, wanda na wani ajin makaranta ne ya fadi ne da misalin karfe 7:30 na daren Litinin.

Majiyoyi a yankin sun ce ginin ya zube ne bayan wani mamakon ruwan sama da aka tafka a yankin a ranar Lahadi.

Galibin wadanda ke zaune a sansanin dai wadanda rikicin ta’addancin Boko Haram ya raba da muhallansu ne.

A cewar Musa Kaka, wani jagoran ’yan sa-kai a garin, “Mutum bakwai ne suka rasu, sannan mutum biyu suka jikkata, kuma yanzu haka suna can a kwance a asibiti.”

Garin na Monguno dai na da nisan kilomita 135 daga Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Hatsarin ya faru ne a wata makarantar sakandare da aka mayar sansanin ’yan gudun hijira, inda kusan mutum 5,000 ke amfani da ita a matsayin matsuguni.

Shi ma wani dan sa-kan, Bello Adamu, ya ce a baya an taba yin gobara a azuzuwan, wacce ta rage musu karfi, kafin daga bisani kuma ruwan ya yi musu illa.

Tuni dai aka yi jana’izar dukkan mutum bakwan a ranar Talata.

(AFP)