Gini ya kashe mutum shida tare da jikkata wasu da dama

Sun dai rasu ne sakamakon wani gini da ake  tsaka da ginawa ya faɗo musu a daidai lokacin da ake tafka ruwan sama a ranar Juma’a.

Gini ya kashe mutum shida tare da jikkata wasu da dama

Ginin da ya rufta

Kimanin mutane shida ne suka riga mu gidan gaskiya a unguwar Jakada Ɗorayi a yankin Karamar Hukumar Gwale a Jihar  Kano.

Sun rasu ne sakamakon  wani gini da ake  tsaka da ginawa ya faɗo musu a daidai lokacin da ake tafka ruwan sama a ranar Juma’a.

Aminiya ta rawaito cewa mutanen da ginin ya yi ajalinsu  sun haɗa da  maigidan tare da ɗansa waɗanda suka zo don duba ginin da kuma ma’aikatan da ke aikin ginin.

Haka kuma ginin ya jikkata wasu mutane da da dama waɗanda suka haɗa da mutanen da suka fakewa ruwan. Mutanen dai a yanzu

a yanzu haka suna kwance a Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed suna karbar magani.

Malam Auwalu Ahmad shi ne mai unguwar Jakada Ɗorayi Babba ya yi wa Aminiya ƙarin haske inda ya bayyana cewa yawancin mutanen da abin ya shafa mazauna yankin ne waɗanda ke neman abinci a wurin.

Mai unguwar ya ce yayin da lamarin ya abku sun garzaya da mutanen zuwa Asibitin Ƙwararru na Murtala Mohammed inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo

China za ta sayar wa Elon Musk TikTok saboda rashin tabbas

Hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru zuwa kashi 34.80 — NBS