Gini ya rufta kan mazauna a Abuja

Lamarin ya faru ne sa’o’i 24 bayan da ginin wata makaranta ya rufta kan ɗaliban da ke rubuta jarrabawa a Jos.

Gini ya rufta kan mazauna a Abuja

Ana fargabar cewa a halin yanzu mutane da dama sun maƙale a ƙarƙashin baraguzan wani ginin bene mai hawa biyu da ya rufta a unguwar Kubwa da ke Abuja a safiyar ranar Asabar.

Kawo yanzu babu wasu cikakkun bayanai dangane da faruwar lamarin, amma wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun ce ginin da abin ya shafa ya rufta ne da misalin ƙarfe 7 na safe.

Bayanai ce masu bayar da agajin gaggawa na kan hanyarsu ta zuwa wurin da lamarin ya faru a yayin da hotuna da bidiyo suka nuna yadda jama’a ke ƙoƙarin ceto wadanda abin ya shafa.

Ginin da ya rufta a unguwar Kubwa da ke Abuja.

Wannan lamari dai ya faru ne sa’o’i 24 bayan da ginin wata makaranta ya rufta kan ɗaliban da ke rubuta jarrabawa a Jos, babban birnin Filato.

Aƙalla mutane 22 ne suka mutu sannan 132 suka samu raunuka kamar yadda wata sanarwar da gwamnatin Jihar Filato ta fitar a daren Juma’a.

NCC ta amince wa kamfanonin sadarwa ƙara kuɗin kira da data

Amurka jinsin mace da namiji kaɗai ta sani a hukumance — Trump

An rantsar da Donald Trump a matsayin Shugaban Amurka na 47

Za mu yi gwanjon motoci 891 da muka ƙwace — EFCC